Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Khalid Saeed al-Batarfi

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Khalid al-Batarfi babban dan kungiyar AQAP ne a Handramaut ta kasar Yemen kuma tsohon dan majalisar shura ne ta kungiayr AQAP. Acikin shekarar 1999, yayi tafiya zuwa kasar Afghanistan, inda yayi aikin horarwa a sansanin al-Farouq na al-Qa’ida. Acikin shekarar 2001, ya yaki sojojin Amurka da Sojan Kawance na Arewaci (Northern Alliance), tare da ‘yan kungiyar Talban, a cikin shekara ta 2010, al-batarfi ya shiga kungiyar AQAP a kasar Yemen, ya jagoranci mayakan AQAP wurin kame gundumar Abyan dake Yemen, kuma aka nada shi Emiyan AQAP na Abyan. Bayan mutuwar shugaban AQAP Nasir al-Wuhayshi a wani harin sama na sojojin Amurka cikin watan Yuni na shekarar 2016, ya samar da wani bayanin dake gargadin cewa al-Qa’ida zata ragargaza tattalin arzikin kasar Amurka da sauran ra’ayoyinta.

Bayan da kasar Amurka ta bada sanarwar cewa za ta amince da kasancewar birnin Jerusalem a matsayin babban birnin Isra’ila, al-Batarfi ya bayyana a cikin wani faifan bidiyon AQAP da aka fitar ranar watan Janairu na shekarar 2018, yana barazana ga gwamnatin Amurka da Yahudawa. A ranar 23 ga watan Janairu na shekarar 2018, Sashen Harkokin Wajen gwamnatin Amurka ta ayyana al-Batarfi a matsayin Danta’addar Kasa- da- Kasa na Musamman (SDGT) kamar yadda Dokar zartarwa mai lamba 13224 ta tanada.

Karin Hotuna

al-Rimi and Batarfi English PDF
al-Rimi and Batarfi Arabic PDF
AQAP English PDF
AQAP Arabic PDF