Labarin kan nasara

Khadaffy Janjalani

Marigayi

Khadaffi Janjalani daya ne daga cikin manyan shugabannin Kungiyar Abu Sayyaf, wata kungiyar ‘yan kishin Islama masu matsanancin ra’ayi da mazauninta ke a kasar Phillipines. Janjalani ne ke da alhakin sacewa da kisan gillar da aka yi wa ‘yan kasashen Amurka da Philippines. An alakanta shi da sacewar da aka yi wa Martin da Gracia Burnham da wasu Amurkawa guda biyu, kuma shine ake zargi da laifin fille kan Guillermo Sobero, wani dan Amurka. Haka kuma Janjalani ya sha shiryawa da kuma aiwatarda hare-hare barkattai akan kadarorin Amurka. Musamman, shine ake dora wa laifin hare-haren bama-bamman da aka kai akan Opishin Jakadancin Amurka dake Manilla da wanda aka kai akan jirgin ruwan Superferry 14 da wanda aka kai Ranar Masoya ta Valentines wadanda, a hade, suka yi sanadin mutuwa ko jin raunin daruruwan mutane.

Bayanin da wasu jarumawan ‘yan kasar Philippines suka bada a watan Satumbar 2006 ne ya taimakawa mayakan rundunar sojan Philippines ta AFP suka ja daga da Khadaffy Janjalani har suka kashe shi. A wattanin da suka biyo baya, an yi ta baza jita-jitar mutuwar Janjalani amma ba tabbacinta tunda jami’an gwamnati basu tabattarda gawarsa ba. A cikin watan Janairun 2007 ne wasu shaidu biyu suka bada bayanai gameda inda gawar Janjalani take wannan kuma binciken likitoci na DNA ya tabattarda cewa lalle da gaske dai Janjalani ya mutu. Bayanan da wadanan mutanen suka bada sunyi anfani matuka wajen tabattarda kashe Janjalani da kuma tabattarda gawarsa. Saboda wannan bajintar tasu ne Gwamnatin Amurka ta bada ladar tukucin Dala milyan 5 (kimanin Peso milyan 245) gare su da kuma sauran jami’an gwamnatin Philippines da suka taka rawa a cikin aikin, kuma an basu tukuicin ne a wajen wani shagali na bainar jama’a da akayi a Tsibirin Jolo wanda kuma Jakadan Amurka a can Philippines ya jagoranta ran 7 ga watan Yunin 2007.

Abdurajik Janjalani, wan Khadaffy Janjalani ne ya fara kafa Kungiyar Abu sayyafa a farkon shekarun 1990s. Shi Abdurajik Janjalani ya sadu da marigayi Usama Bin Ladin ne a Afghanistan inda suke yakar sojan Rasha, kuma daga lokacin ne shi Abdurajik ya fara tunanin ya kafa tashi kugiyar ta kansa a Philippines. Ita wannan kungiyar ta ASG da aka fara kafa ta a tisibirin Basilan na kudancin Philippines, an kafa ta ne da niyyar nemar wa yankunan Mindanao na yammacin kasar da Sulu cikakken ‘yanci a matsayin wata kasa ta Musulmi. Tun daga shekarun 1990s, kungiyar ASG ta sha kai hare-haren bama-bammai akan kadarorin Amurka da Philippines. Haka kuma a shekaru da dama da suka gabata, kungiyar ASG ta sha anfani da nayoyin satar mutane don tara kudaden gudarda aiyukkanta, indatake auna ‘yan yawon shakatawa da ‘yan kasuwa na kasar. Tuni Ma’aikatar harakokin Wajen Amurka ta kadamarda kungiyar ASG a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda ta kasa-da-kasa wacce kuma ke ci gaba da zama barazana ga zaman lafiyar kasar Philippines.