Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Kashe-kashen Karamin Opishin Jakadanci

Karachi, Pakistan | 8 ga Maris, 1995

A safiyar ranar 8 watan Maris na 1995 ne wata farar motar daukar pasinja tazo dauke da ma’aikatan da zsu je bakin aiyukkansu a Karamin Opishin Jakadancin Amurka dake Karachi, Pakistan. Lokacinda tazo kan wani wuri da hanyoyi suka gitta shi ne wata motar taksi mai launin dorawa tazo ta shige gaban motar, yayinda wata mota ta biyu ta tsaya gabanta, ta hana motsi. Daga nan wasu ‘yan ta’adda dauke a makamai suka fito cikin sauri, suka bude wuta kan motar pasinjan, suka yi mata ruwan albarussai, har suka farfasa tagoginta. Ma’aikatan jakadancin Amurka biyu suka rasa rayukkansu a cikin haron, daya kuma ya sai rauni.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.