Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Dakarun juyin juya halin Musulunci

Ma’aikatar Harakokin wajen Amurka za ta bayar da ladar kuɗi har dala miliyan $15 ga duk wanda ya bayar da bayanan da suka taimaka ga dagule harakokin kuɗi na Dakarun juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) da dukkanin bangarori, haɗi da dakaru na musamman na IRGC-Quds. IRGC ta ɗauki nauyin tallafawa hare-hare da ayyukan ta’addanci a sassan duniya. IRGC-QF ke jagorantar ayyukan ta’addancin Iran a wajen Iran ta hanyar wakilanta kamar Hizballah da Hamas.

Ma’aikatar za ta bayar da ladar kuɗi ga bayanai kan hanyoyin samun kuɗi na IRGC, IRDC-QF da rassanta ko kuma hanyoyin da ta ke samun kuɗi da suka haɗa da:

  • Tsarin samun kuɗin IRGC ba bisa ka’ida ba, haɗi da kuɗin mai;
  • Kamfanonin ɓoye masu alaƙa da IRGC da ke gudanar da ayyuka a sassan duniya a madadinsu;
  • Cibiyoyi ko mutanen da ke taimakawa IRGC don kaucewa takunkuman Amurka da na ƙasashen duniya;
  • Cibiyoyin hada-hadar kuɗi da ke huldar kasuwanci da IRGC;
  • Yadda IRGC ke tura kuɗi da kayayyaki ga ‘yan ta’addanta da mayaƙa da kuma Ƙawayenta;
  • Masu tallafawa IRGC ko masu ba ta kuɗi;
  • Cibiyoyin kuɗi ko na ‘yan canji da ke taimakawa IRGC wajen tura kuɗi;
  • Kasuwanci ko hannun jarin IRGC ko na waɗanda ke tallafa mata;
  • Wasu kamfanonin da ke cinikidomin samar da kayayyaki ko makamai a madadin IRGC; da kuma
  • Shirye-shiryen laifuka da suka shafi mambobin IRGC da magoya bayanta, waɗanda ke amfana da ƙungiyar.

An kafa IRGC ne a 1979 bayan yujin juya halin Iran. Wani ɓangare ne na rundunar sojin Iran, kuma musamman ta hanyar dakarun Quds, IRGC tana taka muhimmiyar rawa tsakanin masu ruwa da tsaki a Iran da ke bayar da umurni da aiwatar da ayyukan gwamnatin na ta’addanci a duniya.

A ranar 15 ga Afilu, 2019, ma’aikatar harakokin wajen Amurka ta ayyana IRGC a matsayin ƙungiyar ‘yan ta’adda ƙarƙashin sashe na 219 na dokar shige da fice da ‘yan kasa. A 2017, Ma’aikatar baitil malin Amurka ta ayyana IRGC a matsayin babbar ƙungiyar ‘yan ta’adda ta musamman ƙarƙashin dokar shugaban kasa ta 13224 saboda ayyukanta na goyon bayan IRGC-QF.

Tun kafa ta shekaru 40 da suka gabata, IRGC ta kasance wajen shirya ayyukan ta’addanci da taimakawa ta’addanci a faɗin duniya. IRGC ke da alhakin kai hare-hare da dama kan Amurkawa da ƙadarorin Amurka, haɗi da waɗanɗa suka kashe Amurkawa. IRGC ta taimaka wajen kai hare-hare kan Amurka da dakarun ƙawance da ofisoshin jekadanci a Iraƙi da Afghanistan.

Bugu da ƙari, ƙungiyar ta yi garkuwa tare tsare da kama Amurkawa da dama, yawancinsu ana tsare da su yanzu haka a Iran a yau.

IRGC-QF ta shirya ayyukan ta’addanci a sassan duniya, a ƙasashe kamar Jamus, Bosniya, Bulgaria, Kenya, Bahrain, Turkiyya, da kuma Amurka.

Abdul Reza Shahla’i

Abdul Reza Shahla’i

Jami’in IRGC a Yemen

Abdul Reza Shahla’i ya kasance babban kwamanda na Hukumar IRGC-Qods wanda ta kasance a Sanaa da ke Yemen. Shahla’i yana da daɗaɗɗen tarihi na mummuniyar aniya kan Amurkawa da ƙasashen da ke ƙawance da Amurka.

Shahla’i ya shirya kisan kai daban-daban a kan jami’an haɗin guiwa a Iraƙi. Ya samar da makamai da abubuwa masu fashewa ga ƙungiyoyin Shi’a da ke da zazzafan ra’ayi. Shi ne kuma ya shirya harin da aka kai ranar 20 ga watan Janairu, shekarar 2007 a Karbala da ke Iraƙi wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Amurka guda biyar tare da jikkatar wasu guda uku.

A matsayinsa na mai samar da tallafin kuɗi, sannan babban jami’in IRGC, Shahla’i ya fitar da kuɗi dala miliyan 5 tare da shirya kisan kai a kan Ambasadan Saudiya da ke Washinton DC a shekarar 2011. Baya ga haka, Shahla’i yana shirya hare-hare a cikin Amurka da wasu wurare.

Hukumar Kula da Tattalin Arziki ta Amurka ta bayyana Shahla’i a matsayin Ɗan Ta’addan Duniya na Musamman (SDGT) a shekarar 2008 da 2011. Bayan nan Saudiya da Ƙungiyar Tarayyar Turai da Ingila da Baharen duk sun bayyana shi a matsayin ɗan ta’adda na musamman a shekarar 2018.

Sunaye:

Abdol Reza Shahlai

Abdul Reza Shala’i

`Abd-al Reza Shalai

`Abdorreza Shahlai

Abdolreza Shahla’i

Abdul-Reza Shahlaee

Hajj Yusef

Haji Yusif

Hajji Yasir

Hajji Yusif

`Yusuf Abu-al-Karkh’

Ranar Haihuwa:
Wajajen 1957

Wurin Haihuwa:
Iran

Ƙungiyar Ta’addanci:
IRGC-QF

Bayyanawa a Matsayin Ɗan Ta’adda na Musamman:
Hukumar Kula da Tattalin Arziki ta Amurka SDGT – 2008, 2011

Tarayyar Turai, Ingila, Saudiya, Baharen

Wurare:
Sanaa, Yemen

Kermanshah, Iran

Mazaunin Sojoji na Mehran, Yankin Ilam, Iran

Idan kana da wata masaniya game da Abdul Reza Shahla’i, don Allah ka tuntuɓi ofishin jakadancin Amurka mafi kusa ko cibiyar jakadanci ko ta imel [email protected]

Karin Hotuna

Dakarun juyin juya halin Musulunci
Dakarun juyin juya halin Musulunci
Dakarun juyin juya halin Musulunci
Dakarun juyin juya halin Musulunci
Dakarun juyin juya halin Musulunci
Dakarun juyin juya halin Musulunci
Dakarun juyin juya halin Musulunci
Abdul Reza Shahla’i
Abdul Reza Shahla’i
Abdul Reza Shahla’i
Abdul Reza Shahla’i
Abdul Reza Shahla’i