Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Abdikadir Mohamed Abdikadir

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 3

A kasar Kenya ne aka haifi Abdilkadir Mohamed Abdilkadir, wanda kuma aka sani da lakabin Ikrima, a shekarar 1979. Shi mai yi wa al-Shebaab hidimomi ne kuma mai tsara aiyukkanta.

Al-Shebaab reshe ne na mayakan kungiyar Kotunan Islama na Somalia da suka mallaki aksarin duk kudancin Somalia a kashi na biyu na rabin shekarar 2006. Al-Shebaab ta ci gaba da yake-yaken da take a sassan kudanci da kuma tsakiyar Somalia. Kungiyar ta sha daukan alhakin kai hare-haren bama-bammai, ciki harda hare-haren kunar bakin wajen da ake kaiwa a Mogadishu da sassan tsakiya da arewancin Somalia, inda galibi take auna jami’ai da mutanen da ake ganin kawaye ne na Gwamantin Wucingadin Somalia (TFG). Al-Shebaab ce ta kai tagwayen hare-haren nan biyu na kunar bakin waken da aka kai a Kampala a ran 11 ga watan Yulin 2010 wadanda suka hallaka mutane fiyeda 70, ciki harda Ba’Amurke guda daya. Haka kuma kungiyar ta sha hallaka ‘yan hankoron neman chanji, ma’aikatan bada agaji na kasa-da-kasa, tarin shugabannin al’umma da ‘yan jaridu.

A ran 26 ga watan Fabrairu na shekarar 2008 ne Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka ta kaddamarda al-Shebaab a matsayin Kungiyar Ta’addanci ta Kasashen Waje a karkashin Sashe na 219 na Dokar Shige da Fice da Zaman dan Kasa (kamar yadda aka gyara ta) da kuma kaddamarda ita a matsayin Kungiyar Ta’addanci ta Duniya a karkashin Dokar Hukuma mai lamba 13224 a ran 29 ga watan Fabrairu, 2008. A watan Fabrairun 2012 ne al-Shebaab da al-Qaida suka bada sanarwar hadewarsu.