Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Ibrahim Salih Mohammed al-Yacoub

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

A raar 25 ga watan Yunin 1996 ne ‘yan kungiyar Saudi Hizballah suka kai harin taaddancin akan Gidajen Khobar dake kusa da Dhahran, Saudi Arabia. A wannan lokacin, sojojin Amurka na zaune a cikin wadanan gidaje. ‘Yan ta’addar sun tuka wata mot ace da aka shake da nakiyoyi, suka fasa ta, suka nakkasa ta kwata-kwata illa wani gine da yafi kusa da ita. Wannan farmakin ya hallaka sojojin Amurka 19 da wani dan kasar Saudi Arabia daya; ya kuma raunana mutane 372 daga kasashen duniya daba-daban.

Wannan mutmen da yake a sama, an yanke mishi hukuci a Gundumar Gabashin Virginia kan hannunsa a cikin harin da aka kai ran 25 ga watan Yunin 1996 kan Gidajen Khobar dake Dhahran a Saudi Arabia.

Ana tuhumar wannan mutum da aka nuna a sama da wadanan laifukkan:

Kulla makircin kashe Amurkawa; kulla makircin kashe ma’aikatan Amurka; makiricin anfani da makaman kare dangi akan ‘yan Amurka; makircin nakkasa dukiyoyin Amurka; makircin kai hari kan ma’aikatun tsaro na kasa; harin bam-bammai da aka mutu a cikinsa; anfani da makaman kare dangi kan ‘yan Amurka; yin kisan kai a yayinda ake anfani da wani maganadisu mai janyo asara a lokacin aikata laifi; kisan ma’aikatan gwamnatin tarayya; da kuma yunkurin kashe ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Karin Hotuna

Ibrahim Salih Mohammed al-Yacoub