Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Husayn Muhammed al-Umari

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Ma’aikatar Harakokin Waje ta amince da a bada tukuicin Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da yasa aka kama ko gurfanarda kowanne daga cikin wadanan mutanen: Husayn Muhammed al-Umari.

Hukumar FBI na neman Husayn Muhammed al-Umari saboda rawar da ya taka a harin bam da aka kai kan jirgin saman kampanin Pan American mai lamba 830 a ran 11 ga watan Agustar 1982, wanda ya haddasa mutuwar pasinja daya da jin raunin pasinjoji 16 da kuma yunkurin hallaka matafiya 267 da ma’aikatan jirgin dake cikin jirgin. Al-Umari daya ne daga cikin mutane ukkun da aka yi zargi da aikata wannan ta’addanci kuma an ce ma shine ya zayyana kuma ya hada bam din da ya tashi a cikin jirgin lokacinda yake tafiya daga Narita, Japan zuwa Honolulu, Hawaii.

A Kotun Tarayya ta Gundumar Columbia ne aka tuhumci Al-Umari da aikata wadanan laifukkan: (1) Kitsa makricin gallazawa da nakkasa dukiya, (2) makircin yin kisan kai, (3) kisan kai, (4) bata jirgin sama, (5) bata jirgin saman da ake anfani da shi wajen kasuwanci, (6) girka bama-bammai a cikin jirgin sama, (7) gallazawa, (8) yunkurin bata jirgin sama, da kuma (9) bada tallafi da taimako wajen aikata laifukkan. A shekarar 1998 ne aka kamo kuma aka dawo da Mohammad Rashed, wanda ya taimaka wajen girka bam din a cikin jirgi, nan Amurka. Ya amsa laifinsa ya kuma sanya hannu akan yarjejeniyar bada hadin kai a matsayin amsar da ya shigar dangane da aikata laifin.

Shi dai al-Umari, wanda ake karfafa zaton cewa gwanin kera bama-bammai ne kuma wanda ya taba zama shugaban kungiyar ‘yan ta’adda ta “May 15”, Gwamnatin Faransa ta taba zarginsa ga laifin taka rawa a harin bam da aka kai kantin Marks da Spencer dake Paris da kuma Bankin Leumi a shekarar 1985.

Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka ta bada iznin a bada goron tukuicin da zai kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da ya kai ga kama gurfanar da Husayn Muhammed al-Umari.

Karin Hotuna

Husayn Muhammed al-Umari