Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Harin Bam kan Jami'ar Hebrew

Kudus | 31 ga Yuli, 2002

A ran 31 ga watan Yulin 2002 ne wani bam ya tashi a dakin cin abinci na Jami’ar Hebrew dake Kudus. Wannan fashewar ta hallaka mutane tara cikinsu harda Amurkawa biyar, ta kuma ji wa 85 rauni. Maharan sun yi aiki ne da umurnin shugabannin Hamas, wata kungiyar ‘yan kishin Islama masu tsananin ra’ayi dake zaune a yankunan Palesdinawa.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.