Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Hassan Afgooye

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Hassan Afgooye yana kula da hadaddun cibiyar sadarwa na kuɗaɗe wanda ayyukan su ya haɗa da agaji na karya da rokan kudi, da samun kuɗi ta hanyar haram, da kuma sace mutane cikin goyon bayan duk ayyukan al-Shabaab. Afgooye ya kasance cikin shugabanni na mussamman cikin al-Shabaab kuma yana ƙara karfin su ci gaba da gudanar ayyukan da su ke yi.