Labarin kan nasara

Hamsiraji Marusi Sali

Marigayi

Hamsiraji Sali, kwamanda kuma shugaban wani rukuni na Kungiyar Abu Sayyaf, na da hannu a cikin sacewar da aka yi Jefferey Schilling watan Agustar 2000 da kuma sacewar da aka yi wa Dos Palmas a watan Mayun 2001.

A ran 28 ga watan Agustar 2000 ne Kungiyar Abu Sayyaf ta sace wani Ba’murke mai suna Jefferey Craig Edward Schilling. Kungiyar ta nemi yin musayar Mr. Schilling da neman a bata Dala milyan 10 kuma a sako wasu giggan ‘yan ta’adda guda ukku na kasa-da-kasa dake tsare a gidajen kurkukun Amurka; watau ‘yan al-Qaida Ramzi Yousef da Wali Khan sa kuma “Makahon Sheikh”, shugaban addinin Kungiyar Ta’addanci ta Misra mai suna al-Gama’at al-Islamiyya. A ran 12 ga watan Afrilun 2001 ne Jeffery Schilling ya sami nasarar kauce wa masu neman kama shi, wanda bayan haka ne aka maikdo shi Amurka.

A ran 27 ga watan Mayun 2001 ne kungiyar ASG ta sace wasu Amurkawa guda ukku daga wurin shakatawa na Dos Palmas dake aPalawan a kasar Philippines. Sunayen wadanan Amurkawan sune Guillermo Sobero da Martin da kuma Gracia Burnham, wadanda mishan ne na Amurka mata da miji. A ran 11 ga watan Yunin 2001 ne kakakin ASG, Abu Sabaya ya bada sanarwar cewa yasa an kashe Sobero a matsayin “kyautar taya murnar ranar haihuwa” ga shugabar kasar Philippines, Gloria Macapagal-Arroyo. A ran 7 ga watan Oktobar 2001 ne kuma aka tsinto wani kan bil adama da aka tantance cewa na Guillermo Sobero ne. A cuikin watan Yunin 2002 Martin Bumham ya rasa ransa a cikin fadan da aka gwabza tsakanin sojojin Philippines da mayakan ASG; An ji wa Gracia Bumham amma an ceto shi kuma aka maida shi Amurka.

A cikin watan Fabrairun 2002 ne mahukunta a Washington, DC suka yake hukuncin samun Sali da aikata wadanan laifukkan: makircin da ya haddasa mutuwa, satar mutane da kuma laifukka ukku na satar mutane da ya haddasa mutuwa.

An biya tukucin Dala milyan 1 ga wadanda suka bada labarin da yasa aka gano inda Sali yake.