Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Hamad el Khairy

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Hamad el Khairy shugaba ne kuma yana cikin wadanda suka soma kafa kungiyar ta’addanci ta Fafatikar Hadin kai da Jihadi ta Afrika ta Yamma (MUJWA, wacce kuma aka sani da sunan MUJAWO da TWJWA). A karkashin jagorancin Kahiry, kungiyar MUJWA ta sha satar mutane, da kai hare-haren ta’addanci da kuma yin awon gaba da jami’an diflomasiya na kasashen ektare. Shi kansa Khairy da bakinsa ya amsa cewa shine ya sace wasu ‘yan Algeria su bakwai a cikin watan Afrilun 2012 a Mali, kuma ya sha bayyana a cikin fayafayen bidio na MUJWA inda yake barazana ga masu adawa da kungiyar. A cikin watan janairun 2012 ne Khairy ya fada cewa babban makasudin da MUJWA ta tasa wa gaba shine “girka Dokokin Shari’ar Muslunci a dukkan Kasashen Afrika ta Yamma.”

Kafin ya zama babba a kungiyar MUJWA, Kahiry dan kungiyar AQIM ne, inda yake shirya hare-haren ta’addancin da take kaiwa a Mauritania. A watan Oktobar 2011 ne Kahiry ya bada umurnin a sace wasu Turawa ma’aikata su ukku a Alegria, inda har aka raunana biyu daga cikinsu da harbi. A ran 7 ga waan Disambar 2012 ne aka kaddamarda Kahiry a matsayin Rikakken Dan Ta’adda a karkashin Dokar Hukuma mai lamba 13224.

A cikin watan satumbar ne aka kirkikiro kungiyar MUJWA daga cikin kungiyar al-Qaida a kasashen Islama na Maghreb (AQIM) da manufar fadada aiyukkan ta’addancin da ake a cikinkasashen Afrika ta Yamma. Kungiyar MUJWA ta sha tapka aiyukkan ta’addanci barkattai da sace-sacen mutane, ciki harda harin kunar bakin waken da aka kai a Tamanrasset, Algeria a cikin watan Maris na 2012,wanda ya runana mutane 23. Haka kuma MUJWA ta dauki alhakin sace Jakadan Canada a Majalisar Dinkin Duniya, Robert Fowler a ran 7 ga watan Disambar 2012, kuma a ran 5 ga watan Disambar 2012 ne Kwamitin Ladabtarda al-Qaida na majalisar Dinkin Duniya ya kaddamarda Khairy a matsayin Dan Ta’adda saboda alakarsa da AQIM.