Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Hafiz Saeed

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 10

Hafiz Mohammad Saeed tsohon malamin jami’a ne mai koyar da Larabci da Injiniyanci, kuma yana cikin wadanda suka fara kafa kungiyar Jamaat-ud-Dawa, wata kungiyar ‘yan kishin Islama masu matsanancin ra’ayi na Ahl-e-Hadith da ke da burin shimfida tsarin Shari’ar Musulunci a sasan kasashen India da Pakistan, da kuma bangarenta na mayaka, Lashkar-e-Tayyiba. Ana tuhumar cewa Saeed ne ummul-haba’isin shirya kai tarin hare-hare, ciki harda wanda aka kai a shekarar 2008 a Mumbai inda aka kashe mutane 166, ciki harda Amurkawa guda shidda.

Junhuriyar India ta bada samamcin ‘Yansandan Kan Iyaka na su kamo Saeed saboda rawar da ya taka a harin da aka kai a Mumbai a shekarar 2008. Haka kuma Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta kaddamarda Saeed a matsayin Dan Wata Kasa na Musamman a karkashin Dokar Shugaban Kasa mai lamba 13224. Ita ma Majalisar Dinkin Duniya ta baiwa Saeed Kadamarwa ta Musamman a karkashin Kuduri mai lamba UNSCR 1267 a cikin watan Disamban 2008.

A cikin watan Disambar 2001 ne aka kaddamarda kungiyar Lashkar-e-Tayyiba a matsayin Kungiyar Ta’addanci ta Kasashen Waje. Ita ma kungiyar Jamaat-ut-Dawa a watan Afrilun 2008 ne aka kaddamarda ita a matsayin Kungiyar Ta’addanci ta Kasashen Ketare, kamar yadda ita ma Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamarda Jamaat-ud-Dawa a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda a watan Disambar 2008.