Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Hafiz Abdul Rahman Makki

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 2

Hafiz Abdul Rahman Makki shine na biyu a shugabancin kungiyar Lashkar-e-Tayyiba, wata kungiyar ‘yan kishin Islama masu tsatsauran ra’ayi ta Ahl-e-Hadith da babban burinta shine shimfida dokar Shari’ar Muslunci a wasu sassa na India da Pakistan. Ana zargin cewa kungiyar Lashkar-e-Tayyiba ce ta kai hare-haren nan na watan Nuwamban 2008 a Mumbai wanda mutane 166 suka hllaka a cikinsa, ciki harda Amurkawa shidda da kuma sauran tarin hare-haren da aka kai a India.

Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta kaddamarda Makki a matsayin Wani Fitaccen Dan Kasa a karkashin Dokar Hukuma mai lamba 13224.

A cikin watan Disambar 2001 ne aka kaddamarda kungiyar Lashkar-e-Tayyiba amatsayin Kungiyar Ta’addanci ta Kasashen Waje. Ita ma kungiyar Jamaat-ut-Dawa a watan Afrilun 2008 ne aka kaddamarda da ita a matsayin Kungiyar Ta’addanci ta Kasashen Ketare, kamar yadda ita ma Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamarda Jamaat-ud-Dawa a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda a watan Disambar 2008.