Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Gulmurod Khalimov

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 3

Tsohon Kanar na Sojan Tajikistan, kwamandan ‘yansanda, gwanin harbi na soja, Gulmurod Khalimov, jami’in Kungiyar ‘yan Islama ta ISIL ta Iraq da Levant ne kuma mai daukar mata ma’aikata. Shi ne babban kwamnadan wata bataliyar soja ta musamman da aka kafa a cikin Ma’aikatar Harakokin Cikin Gida ta Tajikistan. Khalimov ya taba fitowa cikin wani faifan bidiyon farfaganda da aka yi, inda aka ganshi yana tabattarda cewa lalle shi mayakin ISIL ne kuma har, a bainar jama’a, yana kira ga a kai wa Amurkawa farmaki na ta’addanci.

A ran 29 ga watan Satumban 2015 ne Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka ta ayyana Khalimov a matsayin Rikakken Dan Ta’adda na Duniya a karkashin Dokar Iko mai Lamba 13224. Haka kuma Kudurorin Majalisar Dinkin Duniya masu lambobi 1267/1989/2253 masu alaka da ISIL (Da’esh) da Kwamitin Takunkumman al-Qaida sun dada cusa shi cikin jerin sunayen mutanen da aka kargafawa takunkumi a watan Fabrairun 2016. Gwamnatin Tajikistan na neman Khalimov.

Karin Hotuna

Gulmurod Khalimov
Gulmurod Khalimov
Gulmurod Khalimov
Gulmurod Khalimov
Gulmurod Khalimov - English