Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Kisan John Granville da Abderahaman Abbas Rahama

Khartoum, Sudan | 1 ga Janairu, 2008

A ran 1 ga watan Janairun 2008 ne aka harbe kuma aka kashe Ba’Murke kuma ma’aikacin Hukumar Raya Kasa ta Amurka (USAID) John Granville da direbansa dan kasar Sudan, Abdelrahman Abbas Rahama a lokacinda suke kan hanyarsu ta komawa gida bayan bikin Jajibirin Sabuwar Shekara da suka halarta a Khartoum, Sudan. A rarrabe, kungiyoyi biyu suka dauki alhakin kai wannan harin: Ansar al-Tawhid (Magoya bayan Akidar Kadaicin Allah Guda) da kuma al-Qaida a Kasar Tapkunan Nilu Biyu (AQTN).

Hukumomin shara’ar Sudan sunyi wa mutane biyar shara’a kuma sun yanke musu hukunci akan rawar da suka taka cikin wadanan kashe-kashen. An yanke hukuncin kisa ta hanyar ratayewa akan Abu Zaid Mohamed Hamza, Mohamed Makawi Ibrahim Mohamed, Abdelbasit Alhaj Alhassan Haj Abdelraouf Hamad, da kuma Mohanad Osman Yousif Mohamed, sai dai kuma sun gudu shekara daya bayan yanke musu hukuncin. Mohanad ya rasu ne a Somalia cikin watan Mayun 2011, shi kuma Abdeltaouf hukumomi sun sake cafke shi daga baya. Har yanzu ba’a kama Makawi da Abdelbasit ba.

Shi dai Abderahaman Abbas Rahama, dan shekaru 39 da haihuwa, a Juba, Sudan, aka haife shi. A shekarar 2004 ya soma aiki da Hukumar Raya Kasa ta Amurka (USAID) a Reshenta na bada Agajin Gaggawa na Darfur. A watan Nuwamban shekarar 2005 aka dauke shi aiki a matsayin Direban Opishin USAID na Sudan dake Khartoum.

John Granville, dan shekaru 33 da haihuwa, asalinsa daga Buffalo, jihar New York yake. Yafi share shekaru ukku yana aikin karfafa akidojin demokradiya da mulki a Sudan, inda ya yi aikin bada kyautar akwatunan rediyo a kudancin Sudan, yankin da yaki ya maida shi saniyar ware na fiyeda shekaru ashirin, don ilmantarda ‘yan kasa kan ‘yancinsu da kuma taimaka musu shiryawa zabukka masu zuwa. Granville ya taba aikin Bauta wa Kasa a kasar Kamaru daga shekarar 1997 zuwa 1999 wanda bayansa ne aka bashi skolashif na Fulbright don ya iya gudanarda bincike a can Kamaru.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.

Wadanda abin ya shafa

Hoton Abdelrahman Abbas Rahama
Abdelrahman Abbas Rahama
Hoton John Granville
John Granville