Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Harin Bam Akan Ayarin Motocin Diflomasiya na Amurka

Beit Hanoun, Zirin Gaza | 15 ga Oktoba, 2003

Ran 15 ga watan Oktobar 2003 newani bam da ya tashi a cikin mota a bakin wani titi dake Beit Hanoun a Zirin Gaza ya hallaka Amurkawa ukku, ya raunana daya. Daman su wadanda abin ya shafa suna bada kariyar tsaro ce ga wakilan Opishin Manzon Amurka a Yankin Gabas ta Tsakiya dake kan hanyarsa zuwa Zirin Gaza don zantawa da ‘yan Palesdinu masu neman gurbin karo ilmi na Fulbright.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.