Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Fuad Mohamed Khalaf

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Fuad Mohamed Khalaf (Fouad Shongale) ya sha samarwa al-Shebaab tallafin kudade; a watan Mayun 2008 har sau biyu yana shirya taron bude wa al-Shebaab asusu a masallatan Kismayo, Somalia. A cikin watan Afrilun 2008 ne Khalaf da wasu mukarrabai suka yi jagorancin anfani da nakiyoyin da aka girke a cikin motoci wajen kai farmaki akan akan sansanonin Ethiopia da jami’an Gwamnatin Wucingadi (TFG) dake Mogadishu, Somalia. A ciiin watan Mayun 2008, Khalaf da wasu mayaka suka kai hari kuma suka kame wata chaji-opishin ‘yan sanda dake a Mogadishu, inda kuma suka kashe sojoji da yawa, suka raunana wasu. A cikin watan Afrilun 2010 ne Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta saka sunan Khalaf a karkashin Dokar Hukuma mai lamba 13536 saboda tarbaccen da yake bayarwa wajen tashin hankali da kuma kawo tabarbarewar tattalin azriki a Somalia.

Al-Shabaab itace bangare mayaka na Majalisar Kotunan Somalia wacce ta kwace aksarin sassan kudancin Somalia a rabin karshe na shekarar 2006. Al-Shebaab ta ci gaba da gudanarda aiyukkanta na ta’addanci a sassan kudanci da tsakiyar Somalia. Kungiyar ta sha daukan alhakin kai hare-haren bama-bammai barkattai – cikinsu har da na kunar bakin wake – a Mogadishu da tsakiya da arewancin Somalia, inda dsau da yawa takan auna jami’an Gwamnatin Somalia da wadanda ake ganin kamar kawaye ne ga Gwamnatin Wucingadin (TFG) ta Somalia. Mai yiyuwa ne al-Shebaab ce ta kai wasu hare-hare guda biyar na kunar bakin wake da aka kai a watan Oktobar 2008 akan wasu birane biyu na arewancin Somalia, inda aka kashe mutane 26, aka raunana wasu 29. Haka kuma al-Shebaab ce ta kai tagwayen hare-haren kunar bakin wake a Kampalar Uganda a ran 11 ga watan Yulin 2010, inda mutane fiyeda 70 suyka hallaka, ciki harda Ba’Amurke daya. Wannan kungiyar ce ke da alhakin kashe ‘yan hankoron neman sauyi barkattai, ma’aikatan bada agaji, tarin manyan jagabannin jama’a fararen hula da ‘yanjarida. A cikin watan Febrairun 2012 ne al-Shebaab da al-Qaida suka bada sanarwar kulla kawance a tsakaninsu.

AA ran 26 ga watan Fabrairun 2008 ne Ma’aikatar Harakokin Waje Amurka ta kaddamarda al-Shebaab a matsayin Kungiyar Ta’addanci ta Kasashen Waje a karkashin Sashe na 219 na Dokar Shige da Fice da Zama Dan Kasa (kamar yadda aka gyara ta), da kuma kaddamarda da ita a matsayin Kungiyar Ta’addanci ta Musamman a karkashin Dokar Hukuma mai lamba 13224 ran 29 ga watan Fabrairu na 2008.