Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Faruq al-Suri

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Faruq al-Suriis shugaban ƙungiyar ‘yan Hurras al-Din (HAD). Al-Suri babban mamba ne a kungiyar al-Ƙa’ida (AQ), inda ya shafe shekaru yana aiki da ƙungiyar ta ‘yan ta’adda. Ya kasance babban mai bayar da horo tare babban kwamandan AQ Sayf al-Adl a Afghanistan a wajajen 1990 kuma ya horar da mayaƙa a Iraƙi daga 2003 zuwa 2005. An tafa tsare Al-Suri a Lebanon daga 2009 zuwa 2013, daga baya kuma ya zama kwamandan al- Nusrah Front. Ya bar al-Nusrah Front a 2016.

A watan Satumba 10, 2019 ma’aikatar harakokin wajen Amurka ta ayyana shi matsayin dan ta’adda na musamman a duniya karkashin dokar shugaban kasa 13224.

Hurras al-Din bangare ne na ƙungiyar al-Ƙa’ida da ta ɓulla a Syria a farkon 2018 bayan saɓanin da ya sa wasu suka ɓalle daga Hay’at Tahrir al-Sham (HTS), Shugabancin HAD, haɗi da al-Suri sun ci gaba da yin biyayya ga AQ da shugabanta, Ayman al-Zawahiri.

Karin Hotuna

Faruq al-Suri
Salman Raouf Salman - Spanish