Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Faker Ben Abdelaziz Boussora

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Faker Boussora, wanda kuma aka sani da sunan Abu Yusif al-Tunisi, dan kasar Tunisia ne dake da alaka da ‘yan kishin Islama masu yawa dake da tsatsauran ra’ayi. Rikakken dan ta’adda ne na al-Qaida da ya sha alwashin cewa yana son yayi Shahada ta hanyar yin kunar bakin waken akshe kansa. Boussora abokin Abderraouf Jdey ne, dan kasar Tunisia wanda ake zargin dan ta’adda ne kuma ana kyautata zaton cewa sukan yi tafiye-tafiye tare da juna.

A shekarar 1988 Boussora ya bar kasarsu ta Tunisia ya koma Faransa da zama. A shekarar 1991 ya bar Faransa ya koma ya zauna a birnin Montreal na kasar Canada, inda kuma, a cikin shekarun 1990s, ya dinga shawagi tsakanin Canada da kasarshi ta haihuwa, Tunisia. A shekarar 1999 Boussora ya zama dan kasar Canada kuma, a lokacin da yake zaune a Canada din, yakan yawan zuwa Masallacin Assuna dake birnin Montreal.

A shekarar 1999 Boussora ya bar Canada, amma watakila ya kara yin tafiya daya zuwa Afghanistan tsakanin shekarun 1999 zuwa 2000. Ya sami horaswa daga al-Qaida a lokacinda yake can Afghanistan kuma, daga nan, sai ya sake komawa Canada.

Hukumomi suna cikin damuwar cewa mai yiyuwa ne Boussora yayi yunkurin sake komawa Canada ko ya shigo Amurka don ya shirya ko kuma ya shiga cikin wani shirin da ake na kai harin ta’addanci. Tana yiyuwa yana da matsananciyar rashin lafiya, yana cikin rauni sosai, abinda zai iya sa ya rame matuka, har kammanunsa su chanja.