Labarin kan nasara

Edgar Navarro

Marigayi

A cikin watan Fabrairu na 2003 ne kungiyar tsageran FARC suka cafke Thomas Howes, Keith Stansell da March Gonsalves, suka yi garkuwa da su a lokacinda jirgin Amurka da mutanen ukku ke ciki ya fdado a cikin kurmin daji Colombia. A matsayin makircin wannan kamun da suka yi ne kuma tsageran na FARC da ‘yan kanzaginsu suka kashe wasu mutane biyu da su ma suke cikin jirgin, Ba’amurke Thomas Janis da dan kasar Colombia Saje Luis Alcides Cruz.

A ran 19 ga watan Oktoba na 2003 ne aka kashe Edgar Gustavo Navarro (mai lakabin El Mocho), Kwamamdan rukunin ‘yan kundumbalan (TFMC) na Teofilo Forero na Mayakan Juyin-Juya Hali na Colombia (FARC), a cikin kazamin musayar wutar da suka yi da Rundunar Sojan Colombia. Kashe Navarro ya biyo ne bayan labarin da wasu mutane ukku dake fatar samun goron tukuicin da suka ji za’a bayar, suka bada wanda yasa har sojojin Colombia suka je can sansanin TFMC inda aka yi wannan fadan. A cikin wtan Afrilu ne aka baiwa kowanne daga cikin masu bada bayanin goron tukuicin Dala 300,000 saboda rahoton da suka bada wanda ya taimaka wajen kashe Edgar Navarro. Ana dai zargin Navarro da cewa yana da hannu a cikin sacewar da aka yi wa wadanan Amurkawan guda ukku da aka ambata a sama.

Tun 1997 Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka ta aiwatarda FARC a matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda ta Kasashen Ketare. Manufar FARC itace ta yi anfani da karfin tsiya, tashin hankali da sauran laifukka wajen tinkarar duk wata kasa, gweamnati ko mutanen dake da sabanin ra’ayi da ita. Tun akalla farko-farkon shekarun 1960s FARC ke da matsananciyar manufar yin adawa da duk wani abu na Amurka kuma ta sha daukan matakin bata duk wasu manufofi na Amurka, inda har ta taba cewa dukkan jami;an gwamnatin Amurka abokan gaba ne da zata iya auna yio musu lahani. Ko bayan safarar miyagun ababa sha da take, har ila yau FASRC tana auna mutane ta hanyar kwace, sata da kisan Amurkawa wadanda ke aiki koziyara ko kasuwanci a Colombia da kasashen dake makwaptaka da ita.