Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Sacewa da kuma Kisan Daniel Pearl

Karachi, Pakistan | 23 ga Janairu, 2002

A ran 23 ga watan Janairun 2002 ne aka sace Daniel Pearl a Karachi, Pakistan. Pearl dai dan jarida ne dake wa Jariudar wall Street aiki kuma yana gudanarda bincike ne akan Richard Reid, dan kai harin bam da takalma, wanda ya so ya tarwatsa wani jirgin saman kasa-da-kasa kamar wata daya kafin a kashe shi Pearl din.

A rabn 21 ga watan Fabrairun 2002 ne aka nuna wani faifan bidio a duniyar gizo ta internet na yadda aka kashe Daniel Pearl. A cikin watan Mayu aka gano gawar Pearl kuma aka maido ta Amurka

Wata daya bayan hakan ne aka tuhumci Ahmed Omar Saeed Sheikh da wasu mutane ukku da da laifin kisan kai saboda rawar da suka taka a cikin sacewa da kisaan Pearl. Ran 15 ga watan Yulin 2002 ne, a Pakistan, aka yanke musu hukunci a kasar Pakistan, inda aka yanke wa shi Sheikh hukuncin kisa.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.