Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Hari akan Masu yawon Bude Ido

Lambun Bwindi, Uganda | 1 ga Maris, 1999

A ranar 1 ga watan Maris na 1999 ne wasu sojojin Interhamwe suka abkawa ‘yan yawon shakatawa dake cikin Lambun “Bwindi Impenetrable National Park” dake Uganda. Ita wannan kungiyar ta Interhamwe wasu zaratan matasan HJutu da suka aiwatarda kisan kiyashin Rwanda a shekarar 1994 ne suka kafa ta.

A cikin wannan farmakin da aka kai a Lambun Bwindi, an kuntatawa masu yawon shakatawa da dsama, wasu anyi garkuwa da su sannan aka tilasta musu yin tattaki zuwa Junhuriyar Demokradiyar Congo. Wani dan Uganda mai suna Paul Ross ma kone shi aka yi, kurumus. Sannan takwas daga cikin maziyartan da suka hada da Amurkawa Susan Miller da Robert Haubner, dukasu aka yi har suka mutu.

An sace tarkaccen kayan maziyartan da dama da suka hada da fasfo na Amurka, Lasisin mota na Amurka, agogon mata na “Citizen Dive” da kuma karamar komputar Toshiba bau’in Portogo

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.