Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Harin ta’addanci akan Opishin Jakadanci da Gidaje na Amurka

Benghazi, Libya | 11-12 ga watan Satumba, 2012

Tsakanar rannakkun 11-12 ga watan Satumbar 2012 ne aka kashe Amurkawa guda hudu – da suka hada da Jakadan Amurka a Libya John Christopher Stevens, da Jami’in Sarrafa Labarai na Ma’aikatan Kasashen Waje Sean Smith, da Dogarawa biyu Glen Anthony Doherty da Tyrone Snowden Woods – a cikin Harin da aka kai a Opishin Jakadanci da Gidaje na Amurka dake Benghazi, Libya. An gudanarda hare-hare da suka hada anfani da tarkaccen makamai iri-iri da suka hada tada gobarar ganganci, manyan bindigogi, gurnetocin da ake cillawa da rokoki (RPGs) da manyan bama-bammai akan ma’aikatu biyu na Amurka dake Benghazi da kuma akan ma’aikatan Amurka dake kan hanya tsakanin wadanan ma’aikatun guda biyu. Ko bayan hakan, wadanan hare-haren sun raunana ma’aikata biyu ‘yan Amurka fa wasu dogarawa ukku ‘yan Libya, sun kuma janyo nakkasa wadanan ma’aikatun guda biyu.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 10 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.

Shi dai jakada John Christopher Stevens dan shekaru 52 da haihuwa, a arewancin jihar California aka haife shi kuma ya fara aikinsa na diflomasiyar kasashen waje ne a shekarar 1991. Jakada Stevens yayi aiyukka a wurare da dama, kuma ya taba zama Mataimakin Shugaban Opishin jakadancin Amurka dake Libya daga shekarar 2007 zuwa 2009. Daga watan maris na 2011 har zuwa watan Nuwamban 2011, Jakada Stevens ya rika mukamin Wakili na Musamman a cikin Majalisar Zartaswa ta Gwamnatin Wucingadi ta Libya, kuma ya iso birnin tripoli ne a watan Mayun 2012 a matsayin Jakadan Amurka a Libya. Kafin ya shiga aikin diflomasiya, Jakada Stevens wani rikakken lauya ne na fannin harakokin ciniki dake a birnin Washington, DC, ya kuma taba zama malamin koyarda turancin Ingilishi na Shirin Bauta wa Kasa na ganin dama a kasar Morocco daga shekarar 1983 zuwa 1985. Sakatariyar harakokin Wajen Amurka Hilary linton ta bayyana Jakada Stevens da cewa shi “namijin duniya ne, mutumen kirki, gwanin fasahar diplomasiya, kuma jarumin Amurkawa.”

Sean Smith, dan shekaru 34 da haihuwa, a birnin san Diego na jihar California aka haife shi kima ya shiga Rundunar Sojan Jiragen Sama ne a shekarar 1995, inda yayi aikin kanikancin hanyoyin sadarwar radio, ya kuma rika mukamin Staf-Saje. A cikin shekarar 2002 ne Smith ya shiga aikin Aiyukkan Kasashen Ketare a matsayin Jami’in Sarrafa Labarai, inda yayi aiki a ma’aikatun kasashen ketare dake birane da dama da suka hada da Baghadaza, Pretoria, Montreal da kuma Hague. A cikin watan Satumbar 2012 ne Smith ya je Benghazi, Libya don yi aiki a fannin sadarwa da mulki a Opishin Jakadancin Amurka na Musamman.

Glen Anthony Doherty, dan shekaru 42 da haihuwa, a Winchester ta jihar Massachusetts aka haife shi kuma ya shiga Rundunar Sojan Ruwa ne a shekarar 19995 inda kuma yayi aiki a kasashen Iraq da Afghanistan. Kafin ya shiga sojan ruwa, Doherty yayi aiki a matsayin malamin koyarda wassanin guje-guje na farar kankara, ya halarci wata makarantar koyon tukin jiragen sama kuma shi kansa kwararren ma’aikacin assibiti ne kuma malamin koyarda tukin jiragen. A cikin shekarar 2005 ne Doherty ya fara aiki da wani kampanin dake samarda tsaro ga jami’an Amurka a kasashen ketare. A cikin watan Satumban 2012 ne Doherty yaje Benghazi, Libya, don yin aikin bada tsaro a Opishin Jakadancin Amurka na Musamman dake can.

Tyrone Snowden Woods, dan shekaru 41 da haihuwa, a birnin Portland na jihar Oregon aka haife shi, kuma ya share shekaru 20 yana cikin Rundunar Sojan Ruwa ta Amurka, inda ya sha zuwa fagagen fama a kasashen Somalia, Iraq, da Afghanistan. Haka kuma Woods kwarraren Nas ne mai rajista, kuma ma’aikacin assibiti mai ilmi mai zurfi. A cikin shekarar 2010 ne Woods ya fara aiki da wani kampani mai zaman kansa dake bada tsaro ga jami’an Amurka a kasashen ketare. A watan Satumban 2012 ne Woods ya tafi benghazi, Libya, don yin aikin bada tsaro ga Opishin Jakadancin Amurka na Musamman dake can.

Wadanda abin ya shafa

Hoton John Christopher Stevens
John Christopher Stevens
Hoton Sean Smith
Sean Smith
Hoton Glen Anthony Doherty
Glen Anthony Doherty
Hoton Tyrone Snowden Woods
Tyrone Snowden Woods