Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Aziz Haqqani

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Aziz Haqqani daya ne daga manyan shugabannin Kungiyar Haqqani kuma shi dan’uwa ne ga madugun kungiyar Haqqani, watau Sirajuddin Haqqani. Aziz ya tsunduma sosai cikin shirya aiyukkan yake-yake da kuma zartad da hukunci kan yadda ake kai hare-hare kan iyakoki akan Rundunar Tsaro ta Kasa-da-Kasa (ISAF) da sojan Gwamnatin Junhuriyar Afghanistan. Haka kuma shine babban wakilin ‘yan gidan Haqqani din wajen aiyukkan yake-yake da ake gudanarwa a Kabul da manyan hare-haren da ake kai a ko ina a cikin kasar.