Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Ayman al-Zawahiri

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 25

Ayman al-Zawahiri a yanzu shine yake shugabancin kungiyar ta’addanci ta al-Qaida kuma shi tsohon madugun kungiyar Jihadin Islama ta kasar Misra ne. A Amurka ne aka zarge shi da taka rawa a cikin farmakin bama-baman da aka kai ran 7 ga watan Agustar 1998 akan ma’aikatun jakadancin Amurka dake kasashen Kenya da Tanzania, inda mutane 224 suka hallaka, wasu sama da 5,000 suka jikkata.

Haka kuma ana tuhumar al-Zawahiri da cewa shi da Usama bin Laden da sauran manyan kusoshin al-Qaida ne suka kulla makarkashiyar harin da aka kai kan katafaren jirgin ruwan sojan Amurka mai suna USS Cole a kasar Yemen a ran 12 ga watan Oktoban 2000, wanda a cikinsa aka kashe sojojin ruwan Amurka guda 17, aka raunana wasu 39, da kuma bada taimako wajen shirya harin da aka kaiwa ran 11 ga watan Satumbar 2011, wanda a cikinsa ‘yan ta’addar al-Qaida 19 suka sace jiragen sama guda hudu na daukar pasinja, suka kuma rabka su akan gine-gine da dama – ciki harda jirage biyu da suka tarwatsa Cibiyar Harakokin Ciniki ta Duniya dake New York, da daya da aka rabka a kan ma’aikatar tsaro ta Pentagon dake kusa Washington, DC, yayinda na hudu kuma ya fadi akan wani fegi dake garin Shanksville na jihar Pennsylvania – wadanda, a hade, suka janyo mutuwar mutane kusan 3,000.

Duk da cewa har yanzu al-Zawahiri na jagorancin wani karamin rukuni mai gauni na manyan jagabannin kungiyar da ake kira Hukumar al-Qaida, hadin kan ‘yan kungiyar yayi rauni a ‘yan shekarun nan a sanadin asaran da kungiyar tayi na manyan shugabanninta asakamakon matakan yaki da ta’addanci da ake dauka a kasashen Afghanistan da Pakistan, da kuma bullar wasu sababbin kungiyoyi kamar Kungiyar islama ta Iraq da Levant (ISIL) wacce ta zama kamar wata mafaka a wurin ‘yan ta’addar dake da korafe-korafe. Sai daiduk da hakan, har yanzu kungiyar al-Qaida da rassanta dake kasashen Kudancin Asia, Afrika da yankin Gabas ta Tsakiya, na ci gaba da zama kungiya mai barazana wacce kuma ke nan daram akan bakanta na son ganin ta kai farmaki akan Amurka da kadarorin Amurka dake warwatse a kasashen duniya daban-daban.

Al-Zawahiri dai yana ci gaba da dauka da kuma aika sakkoninsa, yayinda kungiyar ta al-Qaida ke ta kokarin kai hare-haren dake cin tura a shekarun nan akan Amurka da kasashen Turai. Wannan yana nuna kudurin al-Qaida na ci gaba da shirye-shiryen kai hare-hare amma kuma matakan da ake dauka suna hana ta, kuma yana nuna cewa har yanzu tana ci gaba da nerman hanyar kai farmaki akan Amurka ko a cikin gida ko kuma akan kadarorinta da ‘yan kasar dake wasu kasashen ketare.