Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Amir Muhammad Sa’id Abdal-Rahman al-Mawla

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 10

Al-Mawla, wanda kuma aka fi sani da Hajji Abdallah, shine shugaban ISIS na gaba ɗaya. Shine babban jagoran ‘yan ta’adda a ƙungiyar da ta gabaci ISIS, al-Qa’ida a Iraƙi (AQI), kuma a hankali ya dinga samun muƙamai har zuwa wani babban matsayi na mataimakin shugaba a ISIS.

A matsayin sa na ɗaya daga cikin manyan masu faɗa a ji a ISIS, al-Mawla ya taimaka wurin aiwatarwa da kuma halasta sacewa, kashewa da safarar marasa rinjayen addini na Yazidi a arewacin Iraƙi sannan kuma ya jagoranci wasu hare-haren ta’addanci na ƙungiyar a faɗain duniya.

Al-Mawla ya zama shugaban ISIS biyo bayan mutuwar tsohon shugaban ISIS Abu Bakr al-Baghdadi a watan Oktoba na 2019 lokacin wani harin sojin Amurka.

ISIS, wanda kuma aka sani da Da’esh, ta ambaci al-Baghdadi a matsayin “Khalifa” a watan Yuni 2014, lokacin da mayaƙanta suka ƙwace iko da wasu ɓangarori na Siriya da kuma Iraƙi sannan suka ambata abinda ake kira “halifanci” na Muslunci. A wasu shekaru da suka gabata, ISIS ta sami mubaya’a daga wasu ƙungiyoyi masu da’awar jihadi kuma suka mayar da ra’ayin wasu ya zama mai tsauri a duk faɗin duniya, inda suka cusa ra’ayin kai hare-hare a duk faɗin duniya.

Wannan kyauta lokaci ce mai muhimmanci a wurin faɗan da muke da ISIS da kuma rassanta da cibiyoyinta a duk faɗin duniya. Yayinda aka ga bayan ISIS a fagen fama, mun ƙudiri aniyya ta ganowa da kuma nemo shugabannin ƙungiyar ta yadda haɗin gwiwa na ƙasashen duniya da suke faɗa domin murƙushe ISIS za su ci gaba da lalata ɓurɓushin ISIS da kuma daƙile mafarkinta a kan duniya.

Karin Hotuna

Mawla