Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Kisa da sace Amurkawa

Colombia | Fabrairu, 2003

A ran 13 ga watan Fabrairun 2003 ne wani jirgin saman Amurka dake sintirin farautan dillan ababan sha masu sa jaye ya fadi a Caqueta, Colombia. ‘Yan wata kungiyar ‘yantawaye ta Colombia da ake kira FARC sun hallaka wani Ba’Murke mai suna Thomas Janis da kuma wani sojan Colombia Saje Luis Alcides Cruz. Haka kuma ‘yan tawayen sunyi garkuwa da wasu Amurkawa ukku dake cikin jirgin: Marc Gonsalves, Thomas Howes da Keith Stansell.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.

Wannan tayihn bada goron tukuicin har ila ya shafi kwamandojin FARC irinsu Teofilo Forero Mobile Column da sauran ‘yan kungiyar FARC kamar su Carlos Alberto Garcia Camargo (mai lakabin Harmides Buitrago, mai lakabin El Paisa, mai lakabin Oscar Montero); Marley Yurley Capera Quezada (mai lakabin La Pilosa); da kuma Pedro Gonzalez Perdomo (mai lakabin Alfredo Arenas, mai lakabin Ignacio).