Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Ali Sayyid Muhamed Mustafa al-Bakri

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Ali Sayyid Muhamed Mustafa al-Bakri dan kungiyar al-Qaida ne kuma gwani ne wajen fasahar hada makamai masu guba da makaman yaki. Shi dan Majalisar al-Qaida Shura ne kuma yana da alakar kut-da-kut da jagabannin al-Qaida irinsu Saif al-Adel da Ayman al-Zawahiri.

Kafin ya shiga al-Qaida, al-Bakri dan kungiyar ta’addanci ta Islamic Jihad ta kasar Masar ce a karkashin jagorancin Ayman al-Zawahiri. Yayi aikin koyarwa a Afghanistan inda yake horad da kuratan mayakan ta’addanci da fasahu kan hada nakiyoyi da makamai masu guba. Haka kuma a watan Disambar shekarar 2000 al-Bakri yayi wani yunkurin da ya ci tura na sace wani jirgin saman pasinja na kasar Pakistan. Mai yiyuwa ne har yanzu yana ci gaba da horad da ‘yan ta’addar al-Qaida da sauran masu matasancin ra’ayi.