Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Ali Atwa

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Shi wannan mutum ana kyautata zaton dan kungiyar ta’addancin Lebanon ce ta Hezbollah.

A ran 14 ga watan Yuli na shekarar 1985 ne ‘yan ta’adda suka sace jirgin saman TWA mai lamba 847 yayinda yake kan hanyarsa daga birnin Athens na kasar Grka zuwa birnin Rome na Italiya. Bayan sun yi shawagi daga wannan wuri zuwa wancan ne, barayin jirgin suka sauka a Beirut na Lebanon inda kuma suka bindige kuma suka kashe gwanin ninkaya kuma sojan jiragen ruwa na Amurka, Robert Stethem, kuma suka yada gawarsa akan fakon filin jirgin saman.

Wannan dan ta’addar na sama, an tuhumce shi da laifin shiryawa da kuma zama daya daga cikin wadanda suka sace wani jirgin saman fasinja a ran 14 ga watan Yunin 1985. Sace wnnan jirgin ya janyo cin mutuncin pasinjoji da ma’aikatan jirgin, da kuma kisan gillar da aka yi wa wani Ba’Murke.

Ana tuhumar wannan mutum da aka nuna a sama da wadanan laifukkan:

Kulla makircin satar jiragen sama, satar mutane, yin sata cikin sararin samaniya da ya janyo kisan kai, yi wa ma’aikatan jirgin sama katsalandan a cikin aikinsu, girka wani abu mai iya fashewa a cikin jirgin sama, mallakar abinda ke iya fashewa a jikin mutumen da yake cikin jirgin, gallazawa pasinjoji da ma’aikatan jirgin, yin sata a cikin sarari da ya jayo kisan kai, sata a cikin sartarin samaniya, satar mutane, yi wa ma’aikatan jirgi katsalandan a cikin aikinsu, saka abu mai fashewa a cikin jirgi, ajiye wani abu mai yin lahani a cikin jirgi, gallazawa mutanen cikin jirgi da niyyar sace jirgin ta hanyar anfani da makami mai hatsari, abinda ya janyo jin rauni, bada tallafi da taimako.