Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Ahlam Ahmad al-Tamimi

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

‘Yar kasar Jordan, Ahlam Ahmad al-Tamimi, wanda kuma aka sani da suna “Khalti” da “Halati,” wani dan ta’addan kungiyar HAMAS ne da ke fuskantar shari’a.

A ranar 9 ga Ogosta, 2001, al-Tamimi ya yi jigilar wani bom da wani dan kunar bakin waken kungiyar zuwa wani wurin dake da cunkuson mutane a Ebarro pizzeria dakeJerussalam HAMAS, inda dan kunar bakin waken ya tayar da bom din wanda ya kashe mutane 15, ciki har da yara bakwai. An kashe Amurkawa biyu a cikin harin – Judith Shoshana Greenbaum, wata malamar makaranta mai shekaru 31 mai juna biyu, daga jihar New Jersey, da Malka Chana Roth, wani yaro mai shekaru15. Sama da mutane 120 suka raunata, wadanda suka hada da wsu Amurkaw hudu. Kungiyar HAMAS ta ce ita ke da alhakin kai harin

A cikin shekara ta 2003, al-Tamimi ya ansa laifinsa na hannu a cikin kai harin a wata kotun dake kasar Isra’ila, kuma aka yanke masa hukuncin zama gidan yari na shekaru 16, don taimaka ma maharin. An sake ta a cikin watan Oktoban 2011, a wani bangaren musayar fursunonin da aka yi a tsakanin Kungiyar HAMAS da kasar Isra’ila. A ranar 14 ga watan Maris na 2017, Sashen Adalci ya bude wani koke kan laifuffuka da bayar da damar kama na kasar Amurka On March 14, 2017, al-Tamimi, ana tuhumar ta da a karkashin dokar Amurka da “hada baki a yi amfani da makamin kare dangi kan Amurkawa dake wajen Amurka, wanda ya yi sakamakon rashin rayukka.” Hukumar FBI ta sa al-Tamimi a cikin jerin ‘yanta’addar da ake nema ruw a jallo, wadda ke da “hatsari kuma mai dauke da miyagun makamai.”

Wata tsohuwar dalibar mai aikin jaridar telebijin na wucin gadi, al-Tamimi ta tuka maharin a mota zuwa wurin da aka kitsa kai harin, bayan ya yi alkawarin kai harin a madadin sashen maharan kungiyar HAMAS, kamar yadda hukumar FBI ta ruwaito. Al-Tamimi, wadda wadda ta shirya da kaddamar da harin Sbarro, ta zabi wurin da aka kai harin ne saboda wurin sayar da abinci ne mai cinkoson mutane. Don kaice ma zargin mutane, ita da maharin sun yi shiga irinta mutanen Istra’ila, kuma ta kai bom din da kanta, wanda aka boye a cikin wani makunshin gurmi, daga garin Yammacin bakin kogi zuwa cikin Jerussalam. Al-Tamimi kuma ta karba laifin tayar da wani karamin bom a wani kantin sayar da cefane dake Jerussalam, ‘yanmakonni kafin kai harin, a matsayin gwaji.

Sashen cikin gida na kasar Amurka ya aiyana kungiyar Hamas a matsayin Kungiyar Ta’addanci ta Kasa da Kasa (FTO), a karkashin dokar Hijira da ‘Yankasanci, da kuma Kungiyar ta Musamman da aka sa ma Ido a Duniya (SDGT), a karkashin E.O. 13224.

Shirin bayar da la’ada na Adalci na tayin tsabar dalar Amurka har miliyan 5 ga duk mutunen da ya ba da wani bayani da zai taimaka wurin kama al-Tamimi ko gabatar da ita a gaban shari’a kan rawar da ta taka a wannan harin, a matsayin tayin bayar da la’ada game da Ta’addanci da ke kawo Cikas ga Sulhun Zaman Lafiya a Yankin Gabas ta Tsakiya na shekarar 1993.

Karin Hotuna

Malka Chana Roth
Malka Chana Roth
Judith Shoshana Greenbaum
Judith Shoshana Greenbaum
Tashin bomb na Sbarro Pizzeria a shekarar 2001
Tashin bomb na Sbarro Pizzeria a shekarar 2001
Ahlam Ahmad al-Tamimi
Ahlam Ahmad al-Tamimi