Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Abubakar Shekau

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 7

Abubakar shine shugaban kungiyar Jama’atul Ah-as-Sunnah il-Da’awati wal-Jihad, wacce aka fi sani da sunan Boko Haram. Kungiyar Boko Haram, wacce sunanta ke nufi “an haramta ilmin boko”, kungiyar ‘yan ta’adda ce dake a Nigeria wacce kuma manufarta shine ta tumbuke gwamnatin Nigeria, ta maye gurbinta da gwamnati mai bin tafarkin Shari’ar Musulunci. Tun karshen shekarun 1990s wannan kungiya take raye a tsare-tsare daban-daban.An sha bada rahoton cewa akwai alaka tsakanin Boko Haram da Kungiyar Al-Qaida ta Kasashen Islama na Maghreb (AQIM), al-Shebaab da reshen al-Qaida na Kasashen larabawa, abinda ke kara karfafa gwiwar Boko Haram na ta kai hare-hare.

A can da Shekau ne na biyu a shugabancin kungiyar amma a watan Yulin 2010 ya fito yace shine shugaban Boko Haram, har yayi barazanar cewa zai fara kai hai akan kadarorin kasashen Yammaci dake Nigeria. A cikin wannan watan ne har ila yau, daga baya, Shekau ya fito yana bayyana kawancensa da al-Qaida, yana kuma yi wa Amurka barazana. A karkashin jagorancin Shekau, kungiyar Boko haram ta kara gwanincewa a aiyukkan da take gudanarwa.

A cikin watan Yunin 2011 ne kungiyar ta fara sakin bama-baman gida (IED) ta cikin motoci, kuma tun daga lokacin take kara anfani da wadanan makaman na IED wajen kai hare-hare akan wurare masu saukin kaiwa farmaki. Harin bam na cikin mota da Boko Haram ta kai ran 26 ga watan Agustar 2011 akan Helkwatar Majalisar Dinkin Duniya dake Abuja, Nigeria ne karon farko da kungiyar ta fara kai mummunan farmaki akan wata ma’aikata ta kasashen Yammacin Turai. Akalla mutane 23 suka hallaka, wasu 80 suka ji raunukka a wannan harin. Wani da yace yana magana da yawun Boko Haram ya fito ya ce sune suka kai harin, har yayi alkawarin shirinsu na kai karin irin wadanan hare-haren akan kadarorin Amurka da Nigeria.

Ran 1 ga watan Mayun shekarar 2012, kasa ga mako daya bayan harin bam da kungiyar ta kai akan kampanin wata jarida ta Nigeria dake Abuja ne, Boko haram ta sako wani sakon faifan bidiyo inda take barazanar kai irin wadanan hare-haren akan kafofin watsa labaran Nigeria da na kasashen ketare, ciki harda Gidan rediyon Muryar Amurka da kafar mujallar “Sahara Reporters” da ake bugawa a duniyar gizo daga birnin New York.

A karkashin jagorancin Shekau, kungiyar Boko Haram ta sha auna kananan yara. A ran 14 ga watan Afrilun 2014 ne, Boko Haram ta sace ‘yanmata kusan 300 daga makarantarsu dake Arewancin Nigeria. A cikin wani faifan bidikyo da suka sako makkoni ukku bayan hakan ne, Shekau ya dauki alhakin sace ‘yanmatan, wadanda ya kira su “bayi”, har yayi barazanar zai saida su a kasuwa.

A ran 21 ga watan Yunin 2012 ne, ma’aikatar harakokin Wajen Amurka ta kaddamarda Shekau a matsayin Rikakken dan Ta’addar Duniya Na Musamman a karkashin Dokar Hukuma mai lamba 13224.