Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Adnan Abu Walid al-Sahrawi

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Adnan Abu Walid al-Sahraoui (Abou Walid) shi ne shugaban kungiyar yan ta’adda mai suna Daular Islamiya a Babban yankin Sahara (ISGS), kuma wadda aka sani da sunan ISIS-GS a takaice. An kafa kungiyar ISIS-GS, bayan wata baraka da ta kunno kai bayan ficewar Abu Walid da magoya bayansa daga bangaren kungiyar Al-Mourabitoun, wanin reshen kungiyar da ya raba gari da uwar kungiyar Al-Qaida.

Abu Walid ya bayyana yin mubayi’a ne a karon farko ga kungiyar ISIS a watan Mayun shekara 2015, kuma kungiyar ISIS din ta karbe shi a watan Oktoba shekarar 2016. Kungiyar ISIS-GS na girke ne a kasar Mali, musamman ma tsawon iyakar Mali da Niger. Kungiyar ISIS-GS ta dauki alhakin kai hare haren ta’addanci da dama a karkshin jagorancin Abu Walid, wadanda suka hada da harin ranar hudu ga watan Oktobar 2017 kan wani ayarin kawancen sojojin Amurka da Niger masu yin sintiri a kauyen Tongo Tongo a kasar Niger kusan iyaka da kasar Mali, harinda ya yi sanadiyar mutuwar sojojin Amurka hudu da wasu sojojin Niger hudu.

A ranar 16 ga watan Mayun 2018, Ofishin Ministan harkokin wajen Amurka ya bayana Abu Walid a matsayin Babban Dan Ta’adda na Duniya , musamman a karkashin wani kudurin bincike mai lamba 13224 , ita kuwa kungiyar ISIS-GS, an ayyana ta a matsayin Kungiyar Ta’addanci ta Kasashen ketare a karkashin kuduri mai lamba 219 na dokar da ta tsara ayyukan shige da fice da ma zaman dan kasa.

Karin Hotuna

Adnan Abu Walid al-Sahrawi
Adnan Abu Walid al-Sahrawi
Adnan Abu Walid al-Sahrawi
Adnan Abu Walid al-Sahrawi
Adnan Abu Walid al-Sahrawi
Adnan Abu Walid al-Sahrawi