Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Abu Ubaidah (Direye)

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 6

Abu Ubaidah (Direye) shi ne shugaban al-Shabaab. Kakakin Al-Shabaab, Ahmed Abdi aw Mohammed, ya sanar da jama’a cewa Abu Ubaidah ne shugaban ƙungiyan a ranar shida na watan Satumba, 2014, bayan mutuwar tsohon al-Shabaab emir Ahmed Abdi aw-Mohammed (Godane). Abu Ubaidah ya kasance daya daga cikin mutanen ciki wanda sun fi yi kusa da Godane a lokacin mutuwar Godane. Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) sun hore masa takunkumi yadda doka cikin sakin layi takwas na Ƙudurin Kwamitin Tsaro na UN ta shekarara 1844 ya wajabta, a ranar ashirin da biyar na watan Satumba, shekarar 2014.

An ce wai yana bin akidun Godane mai cewa al-Shabaab ba ƙungiyar ƙasar Somalia kawai ba, ya fi haka, a maimako shi fuska daya ne cikin yakin jihadi da al-Qaeda ta ke yi a duniya.

Tun da emir, wato Abu Ubaidah shi ne kai tsaye da alhakin ayyukan al-Shabaab, Wanda ta ci gaba da barazana da zaman lafiya, tsaro, da kwanciyar hankali na Somalia da kuma bukatun Amurka a yankin. An ce shi mutum mai shekaru fiye da arba’in ne kuma shi ɗan kabilan Dir ne daga yankin Kismayo a Somalia.