Labarin kan nasara

Abu Solaiman

Marigayi

Abu Solaiman daya ne daga cikin manyan shugabannin ku giyar Abu Sayyaf (ASG), wata kungiyar masu akidar addini sosai a kasar Philippines. A matsayinsa na shugaban shirye-shirye da lura da kayan aiki na kungiyar ASG, Solaiman, tareda Khadaffy Janjalani, sune ke da alhakin sacewa da kuma kashe ‘yan kasashen Philippines da Amurka. An taba alakanta shi da batun sace Martin da Gracia Burnham da wasu Amurkawa guda biyu. Haka kuma Solaiman na cikin wadanda suka fille kan Guillermo Sobero, shima wani Ba’Amurke. Wadanan ba su kadai ne hare-haren da Solaiman ya shirya aka kai ba, don ko bayansu ya sha shirya hare-haren barkattai akan kadarorin Amurka ciki harda farmakin da aka kai akan Opishin Jakadancin Amurka dake Manila da na (jirgin ruwan) Superferry 14 da bama-bamman da aka saka a “Ranar Masoya” ta Valentines wadanda dukkansu, a hade, suka kashe ko suka raunana daruruwan mutane.

A ran 16 ga watan Janairun 2007 ne Rundunar Sojan Philippines, a bisa bayanin da wasu jarumawan ‘yan kasar ta Philippines su biyu suka bada, suka shirya kai samame da kuma kashe Solaiman. Wannan yunkurin yayi nasara kuma an samu nasarar ne kawai saboda bayanin da wadanan mutanen suka baiwa sojan Philippines. Bayanin da wadanan mutanen suka bada ne ya taimaka har aka kai ga gano, kashe da kuma tabattarda gawar Abu Solaiman. Saboda wannan namijin aiki da taimakon da suka bada ne, Gwamnatin Amurka, a wajen wani shagali da Jakadan Amurka ya yi wa jagoranci a ranar 7 ga watan Yunin 2007 a Tsibirin Jono, ta baiwa wadanan mutanen goron tukuici na Dala Milyan 5 (daidai da Peso milyan 245).

Abdulrajik Janjalani, yayan Khadaffy Janjalani ne ya kafa kungiyar Abu Sayyaf a farkon shekarun 1990. Abdurajik Janjalani ya sadu da marigayi Usama Bin Ladin ne a Afghanistan lokacinda suke yakar sojan Tarayyar Soviet, kuma a nan ne ya sami karfin zuciyar yazo ya kafa tashi kungiyar ‘yan kishin Islama a Philippines. Ita kungiyar ta ASG, wacce acan farko aka kafa ta a Tsibirin Basilan dake kudancin Philippines da makasudin neman kafa wata kasar Musulmi zalla a yammacin Mindanao da Tsaunukkan Sulu. Tun daga shekarun 1990s, ASG take kai hare-hare akan kadarorin Amurka da Philippines. Haka kuma a shekarun da suka gabata ASG ta sha kai hare-hare don ta samu tara kudade, inda take auna maziyarta da ‘yan kasuwa. Tuni Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka ta kaddamarda ASG a matsayin kungiyar ta’addanci, kuma tana ci gaba da yin barazana ga zaman lafiyar Philippines.