Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Abu Bakr al-Baghdadi

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 25

Abu Bakr al-Baghdadi, wanda har wa yau aka san shi da lakabin Abu Du’a, da kuma lakabin Ibrahim ‘Awwad Ibrahim ‘Ali al-Badri, shine babban shugaban kungiyar ta’addanci ta Isalama ta Iraq da Levant (ISIL). Barazanar al-Baghdadi ta dada karuwa tun daga shekarar 2011, lokacin da Ma’aikatar Harakokin Waje tayi sanarwar bada goron Dala Milyan 10 ga duk wanda ya bada bayanin da ya kai ga inda yake, kama shi ko kuma kai ga yanke mishi hukunci. A cikin watan Yunin 2014 ne kungiyar ISIL, (wacce kuma aka sani da sunan Da’esh) ta kama sassa daban-daban a kasashen Syria da Iraq, ta girka mulkin Islamiyya kuma ta nada al-Baghdadi a matsayin shugaban addini na wuraren. A shekarun da suka gabata, ISIL ta sami mubayi’ar kungiyoyin ‘yan jihadi da dama da kuma nasarar cusawa mutane akidar addini mai tsanani a kasashen duniya daban-daban, ta kuma karfafa gwiwar a rinka kai hare-hare akan Amurka.

A karkashin jagorancin al-Baghdadi, ISIL ta hallaka dubban mutane fararen hula a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya daban-daban, ciki harda kisan kisan gillar da tayi wa mutanen da ta kama tana garkuwa da su ‘yan kasashen Japan, Ingila da Amurka. Shi kansa al-Baghdadi ya dauki alhakin dimbin hare-haren da aka yi ta kaiwa a Iraq tun shekarar 2011, abinda ya janyo mutuwar dubban ‘yan Iraq fararen hula. Haka kuma kungiyar ta kai hare-hare a yankunan dake wajen yankunan dake karkashin ikonta. A harin da ta ISIL ta kai a watan Nuwamban 2015 a birnin Beirut, mutane 43 ta kashe, ta raunana wasu 239. Har ila yau a cikin wannan Watan ne ISIL ta kai hare-hare har guda bakwai a birnin Paris, inda mutane 130 suka rasa rayukkansu, wasu sama da 350 suka jikkata. A watan Maris na 2016 ne kuma ‘yan ta’addar ISIL suka kai farmaki a Brussels inda suka hallaka 34 – ciki harda Amurkawa hudu – suka kuma raunana wasu sun fi 270.

Ma’aikatar harakokin Waje ta kaddamarda al-Baghdadi a matsayin Rikakken Dan Ta’addar Duniya (SDGT) a karkashin Doka mai Lamba 13224. Haka kuma an saka sunanshi a Kwamitin Horad da ’yan ISIL (Da’esh) da al-Qaida dake wurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Karin Hotuna

Baghdadi Poster 1 - English
Photo of Abu Bakr al-Baghdadi