Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Abu-Muhammad al-Shimali

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Tun cikin shekarar 2005 ake alakanta Tirad al-Jarba da aka fi sani da lakabin Abu-Muhammad al-Shimali, wanda kuma shine Shugaban Harakokin Kan Iyakoki na Kungiyar Al’ummar Islama ta Iraq da Levant (ISIL) da ita kungiyar ta ISIL, wacce a can da aka sani da sunan al-Qaida a Iraq. Yanzu haka shine yake jagorancin aiyukkan da suka danganci Shige da Fice da kuma Samarda Kayan Aikin a kungiyar ISIL, kuma shine yake da hakkin shirya sufurin ‘yan ta’addar kasashen ketare da ake ratsawa da su ta cikin Gaziantep, kasarTurkiyya zuwa cikin garin Jarabulus na kasar Syria, wanda ke karkashin rikon kungiyar ISIL. Shi al-Shimali da Kwamitin Shige da Fice da Samarda Kayan Aiki sune ke gudanarda aiyukkan fasa kwabri, sarrafa aika kudade zuwa wurare da kuma kai kayan aiki zuwa cikin Syria da Iraq, watau kayan da suke daukowa daga kasashen Turai, Afrika ta Arewa da Kasashen Larabawa. Ko a shekarar 2014, al-Shimali ne yayi hidimar bude hanyoyin da aka bi wajen kai sababbin mayakan ISIL daga Turkiya zuwa Syria, wadanda aka dauko su daga Australia, Turai da kasashen Gabas ta Tsakiya, kuma shine ya jagorancin aiyukkan cibiyar daukan sababbin ma’aikata dake Azaz, Syria.

Amurka da Cibiyar Hadin Gwiwa ta Duniya da ta hada abokan aiki fiye da 60 sun dukufa wajen zubar da darajar kungiyar ISIL da kuma samun galaba a kanta a fagen yaki. Sai dai kuma, idan ana son cimma wannan burin, wajibi ne a sami ingantaccen tsari na hadin kai wajen aiki tareda juna da hada karfi. Daya daga cikin matakan da Cibiyar Hadin Gwiwar ke dauka itace ta hanyar dakile hanyoyin sufurin ‘yan ta’addan kasashen ketare. Don cimma wannan makasudi ne aka samu hadin kan kusoshin hukumomin tsaron kasa, ma’aikatun tsaro, shara’a, leken asirai, diflomasiya, soja, kwararru da kuma masanan kafofin watsa labarai, wadanda duk suke aiki da junansu.

Mayakan ‘yan ta’adda fiyeda 25,000 daga kasashen duniya sama da 100 ne suka je Iraq da Syria. Fagagen yaki na kasashen Iraq da Syria sun zama kamar wasu wuraren samarda horaswa a wurin wadanan mayakan inda suke dada kwarewa da fasahun yaki, aiki da makamai da nakiyoyi, kuma suna cudanya da sauran wasu ‘yan ta’adda dake shirin kai hare-hare na gaba akan Kasashen Yammacin Turai. Wannan barazanar kai hare-hare akan wurare masu alaka da juna ta kara karfafa bukatar yin aiki da juna a tsakanin ma’aikatun tarayyar Amurka da na kasashe duniya, wadanda zasuyi anfani da duk wata dama da suke da ita wajen dakile zirga-zirgar mayakan ‘yan ta’adda kuma, a karshenta, suyi nasara a kan kungiyar ta ISIL.