Makaman Kare Dangi

‘Yan ta’addar dake da kudurin samu da anfani da anfani da makaman kare dangi (WMD) babban barazana ne ga zaman lafiyar kasashen duniya. Makaman kare dangi (WMD) na iya hallaka dimbin mutane masu yawa kuma har sukan fi karfin ma’aikatun bada agajin gaggawa. Makaman kare dangi (WMD) sun hada da makaman nukiliya, da wadanda ke kunshe da sinadari mai kisa, da masu sa cuta da masu warwatsa gubar iska da kuma manyan bama-bammai dake iya hadfdasa mummunar barna mai yawan gaske.

Amurka ta daura damarar hana wa ‘yan ta’adda iya yin anfani da wadanan miyagun makamai.

Idan ka bada wani bayani da zai kai ga kama ko hukuntarda duk wani mutumen dake kokarin ko yake hada kai da wasu wajen kokari, ko taimakawa da bada tallafi ga wasu wsajen aikata aiyukkan ta’addancin kasa da kasa da ya hada anfani da miyagun makamai (WMD) akan Amurkawa ko kadarorin Amurka a koina suke a duniya, zaka iya samun goron tukuici.

Kulawa: Duk wani bayanin da aka bada da ba na gaskiya bane, za’a kai rahotonsa ga hukumomin da suka dace.

A ran 15 ga watan Yulin 2006 ne Shugaba Bush da Shugaba Putin suka kaddamarda Shirin Yaki da Ta’addancin Nukiliya Na Duniya. Babban makasudin wannan muhimmin shirin shine don a dada fadada hadin kai da aiki tare wajen yaki da barazanat ta’addancin nukiliya.