Labarai Kan Nasarorin Da Aka Samu

Izuwa yanzu Shirin Bada Tukuici Don Adalci ya biya sama da Dala milyan 150 ga mutane sama da 100 da suka bada bayanan da suka hana ayi ta’addancin kasa da kasa ko taimakawa wajen gurfanarda wadanda suka riga suka aikata ta’addancin a gaban shara’a.

Su ma wasu jarumawa da suka bullo da bayanai, sun taka muhimiyar rawa wajen hana akai hare-hare ko kuma wajen warware yadda aka shirya wasu hare-haren ta’addanci na baya.

  • RFJ ta biya miliyoyin daloli a 2019 wanda ya kai ga gurfanar da daya daga cikin shugabannin ISIS a Gabas Ta Tsakiya.
  • A lokacinda ake yakin Yankin Bakin Tekun Pasha, wani jarumin mutum a daya daga cikin kasashen Asia ta gabas ya bayyana dauke da bayanai gameda wasu hare-haren da aka shirya za’a kai. Ashe daman su ‘yan ta’addan sun riga sun nazarci wuraren da zasu kaiwa farmakin har ma sun hada hancin makaman da zasuyi anfani da su da suka hada da bindigogi, gurentoci da nakiyoyi. Ana saura sa’oi 48 a soma kaddamarda harin ne wannan mutumen ya fito da bayanin da ya bada dama aka tarwatsa shirin nasu. An hana a kai harin, an bada goron tukuici ga wannan matashin sannan an dauke shi da iyalinsa, an sauya musu wurin zama, aka kaisu wani wuri inda zasu zauna cikin natsuwa da kwanciyar hankali. Bayanin da wannan mutumen ya bada ya taimaka matuka wajen ceton daruruwan rayukka.
  • A wani lamarin na daban kuma, wata matashiyar macce ta kawo rahoto kan wasu mutanen da suka sace wani jirgin saman pasinja, suka yi wa mutanen dake cikin jirgin dukan kawo wuka. Tace ita ma kanta “jikinta ya gaya mata” cewa ba zata tsira daga harin ba. Karshenta an kama madugun ‘yan satar jirgin, kuma aka dawo da shi Amurka aka jefa shi kurkuku a bisa laifin satar jiragen sama. An dai baiwa wannan matashiyar maccen goron tukuici don yabawa da kokarinta wajen hana a yi ta’addanci.
  • Wata daliba kuma, a jami’ar wata kasar waje, ta shedi kisan gillar da aka yi wa wani jami’in diflomasiya na Amurka. Sakamakon bayanin da ta bada ne aka yanke hukuncin daurin rai da rai akan mutane biyun da suka kai harin. An sauya wa dalibar da iyalinta wurin zama, zuwa wani wuri mai kwanciyar hankali, kuma an bata goron tukuici.