Bayanin Shirin

A karkashin Dokar 1984 ta Yaki da Ta’addancin Kasa da Kasa mai Lambar Doka 98-533 (da aka tsara a 22 U.S.C. § 2708) ne aka kafa Shirin Bada Tukuici na Tinkarar Ta’addanci na Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka. Makasudin wannan shirin da Sashen Tsaron Ma’aikatun Diplomasiya na Ma’aikatar Harakokin Waje ke gudanarwa, shine don a gurfaarda ‘yan ta’addar kasa da kasa a gaban shara’a don a hukunta su da kuma hana musu kai hari akan Amurkawa ko kadarorin Amurka. A karkashin wannan shirin, Sakataren Harakokin Wajen Amurka na da hurumin bada iznin a bada tukuci ga duk wanda ya taimaka wajen kamawa ko hukunta duk wani da ke kokarin kitsa makirici, ko ya aikata, ko ya taimaka aka aikata ko kuma yayi yunkurin aikata ta’addanci akan Amurkawa ko kadarorin Amurka, ko wanda ya taimaka wajen hana a kai irin wannan farmakin tun fsrko, ko ya taimaka wajen gano ‘yan ta’adda ko mazauninsu, ko kuma ya taimaka wajen wargaza duk wasu hanyoyin samun kudade na ‘yan ta’adda.

An yardarm wa Sakataren Harakokin Waje ya/ta biya tukuicin da ya zarce na Dala milyan 25 idan shi koi ta suka cimma matsayar cewa ana bukatar kudin da ya fi hakan don shawo kan ko tinkarar aiyukkan ta’addanci akan Amurka.

Daga lokacinda aka fara fitowa da Shirin Bada Tukuic Don Adalci a shekarar 1984 zuwa yau, Amurka ta biya tukucin da ya zarce Dala milyan 150 a mutanen fiyeda 100 da suka bada bayanin da aka yi anfani da shi wajen jefa ‘yan ta’adda a kurkuku ko kuma aka hana aikata aiyukkan ta’addanci a duk duniya. Wannan shirin ya taka babbar rawa wajen cafke Ramzi Yousef, ummulhaba’isin harin bam din da aka kai kan Cibiyar Ciniki ta Duniya a shekarar 1993.

Koda yake ana anfani da Shirin Bada Tuykuici Don Adalci wajen hana ta’addanci akan Amurkawa, Gwamnatin Amurka na musayar bayanan da wasu kasashe wadanda mutanensu ke fuskantar barazanar ta’addanci. Kowace Gwamnati da Kowane Dan Kasa suna da hakkin da ya rata a wuyansu na gurfanarda ‘yan ta’adda agaban Shara’a da kuma hana aikata aiyukkan ta’addanci.