Manufofin Rufa Asiri

Sanarwa Kan Dokar Rufin Asiri

Akan tara bayanan alkalumma don gudanarda shafin wannan shirin. Shirin Bada Tukuici Don Adalci yakan yi anfani da fasahu don tsara jadawaloli dake da manufofi iri-iri kamar sanin ko wane bayani ne yafi anfani ko wane ne bai da anfani da yawa, ko don a gane yadda shirin ke aiki ko matsalolin da yake fuskanta. Ga misalin bayanan da aka tara dangane da ziyarar da ka kai a shafin: sunan mashigar Duniyar Gizo ta Internet wacce ta cikinta ka biyo har ka shigo shafin Shirin Bada Tukuici (alal misali kamat shafin “aol.com”, idan ka shigo ta zayren America Online) sannan kuma da rana da lokacinda ka shigo shafin namu.

Don tabattarda matakan tsaro da kuma tabattarda cewa kowa ya ci moriyar wannan shafin, akwai wasu fasahu da ake anfani dasu wajen gano mutanen da ke shigowa shafin namu don a tabattar da cewa an gane mutanen dake kokarin sauko da bayanai bada izni ba ko sauya bayanan dake shafin ko dai haddasa wata barna. An hana duk wani haramtaccen yunkuri n saukarda bayanai ko sauya bayanan dake wannan shafin bada izni ba kma duk wamnda yayi kokarin yin hakan za’a iya mishi horo a karkashin Dokar Hana Zamba da Lalata Kwamputa ta 1986. Ana kuma anfani da bayanan dake wannan shafin saboda binciken da Hukumomin Ma’aikatan Kare Doka ke gudanarwa. Bayan wadanan manufofin da aka fayyace, ba wani anfani da ake da wannan shafin wajen gano masu anfani da shi ko yadda suke anfani da shi din.

Dokar Hana Zamba da Lalata Kwamputa

An hana duk wani yunkuri na saukarda bayanai ko sauya bayanan dake shafin, kuma duk wani yunkuri na yin haka, abu ne da za;a iya karar mutum a gaban shara’a a kansa, a karkashin Dokar Hana Zamba da Lalata Kwamputa ta 1986 da kuma Dokokin Babe na 18 na U.S.C, Sassa na 1001 da 1030.

Hanyoyin zuwa Wasu Shafuna na Daban

Duk hanyoyin da aka tana a wannan shafin wadanda basa da alaka da Gwamnatin Tarayya ta Amurka ko anfani da sunayen kungiyoyin ‘yan kasuwa, kampunnan da aka gani a shafin Shirin Bada Tukuici Don Adalci, an tanade su ne kawai don anfanin masu anfani da shafin. Ganinsu a shafin ba wai yana nufin Ma’aikatar Harakokin Waje ko Shirin Bada Tukuici Don Adalci sun rungumi akidojin wqadanan kungiyoyi da kampunnan masu zaman kansu ko wasu aiyukka ko sana’oi na masu zaman kansu ba.

Tara Bayanai

Muna tara wadanan bayanan:

  • Danna zubowar bayanai
  • Fannonin HTTP

Za’ayi anfani da wannan bayanin saboda wadanan dalilan:

  • Kammalawa da tallafin aikin da ake a yanzu.
  • Gudanarda shafin da tsari
  • Bincike da Gudanarwa

Shirin Bada Tukuici Don Adalci ne da wakilansa zasuyi anfani da wannan bayanin.

An tanadi bayanin nan mai zuwa don bayyana dalilin da yassa ake tara shi bayanin:

  • Shirin RFJ kan tara fayel-fayel dake knshe da wannan bayanin.

Alkakan kwamputa

Alkakan kwamputa wata fasaha ce fz kwamputa dake taimakawa wajen samar maka wani takamammen bayani dafa wani shafi na duniyar gizo ta internet. Wannan alkakin wani bayani ne da wani shafi yake aikawa ga hanyarka ta zagayen duniyar gizo ta internet wanda kuma za’a tanada akan kwamputar taka. Lkana oiya umurtar kwamputarka ta sanarda kai a duk lokacinda ka sami wani alkaki, abinda zai baka damar ka aminta da shi ko ka watsar.

Shafin RFJ baya anfani da alkakan HTTP.

Takaitaccen Bayanin Tsari

Takaitaccen Bayani Tsari wani nau’i na manufar P3P ne wanda ke bada takaoitaccen bayani kan alkakai. Da yake wannan bayani bai ce komai ba gameda alkakai, wannan na nufin ke nan ba wata manufa a nan gameda tsarin.

Manufa na ambatar anfani da alkakai idan har akwai “Alkakan HTTP” a cikin manufar. Wannan bayani ana samunshi a ciki “Dynamic Data”.