Tambayoyi da Amsoshin da aka fi fatawa a kansu

 • Zaka iya bada wani bayani gameda Shirin Bada Tukuici Don Adalci na RFJ?

  Zaka iya bada wani bayani gameda Shirin Bada Tukuici Don Adalci na RFJ?

  • A karkashin Dokar 1984 ta Yaki da Ta’addancin Kasa da Kasa mai Lambar Doka 98-533 (da aka tsara a 22 U.S.C. § 2708) ne aka kafa Shirin Bada Tukuici na Tinkarar Ta’addanci na Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka. Makasudin wannan shirin da Sashen Tsaron Ma’aikatun Diplomasiya na Ma’aikatar Harakokin Waje ke gudanarwa, shine don a gurfaarda ‘yan ta’addar kasa da kasa a gaban shara’a don a hukunta su da kuma hana musu kai hari akan Amurkawa ko kadarorin Amurka. A karkashin wannan shirin, Sakataren Harakokin Wajen Amurka na da hurumin bada iznin a bada tukuci ga duk wanda ya taimaka wajen kamawa ko hukunta duk wani da ke kokarin kitsa makirici, ko ya aikata, ko ya taimaka aka aikata ko kuma yayi yunkurin aikata ta’addanci akan Amurkawa ko kadarorin Amurka, ko wanda ya taimaka wajen hana a kai irin wannan farmakin tun fsrko, ko ya taimaka wajen gano ‘yan ta’adda ko mazauninsu, ko kuma ya taimaka wajen wargaza duk wasu hanyoyin samun kudade na ‘yan ta’adda.

   Shirin RFJ yakan ajiye jerin bayanan duk tukuicin da yake bayarwa a shafinsa na duniyar gizon internet na www.rewardsforjustice.net. Aksarin duk tukuicin da Shirin RFJ ke bayarwa yak an iya kaiwa na dala milyan 5. To amma kuma goron tukuicin na iya kamawa daga Dala milyan 1 har zuwa dala milyan 25. Haka kuma wannan shirin na ma iya biyan wannan tukuicin ko a wuraren da ba’a tanade shi ba, in dai ta kama.

   Daga lokacinda aka kafa shi zuwa yau, Shirin RFJ ya biya mutane fiyeda 100 ladar sama da Dala milyan 150 bayanan da suka bayar da suka hana a kai hare-haren ta’addanci ko kuma suka taimaka wajen kamo wadanda suka taba aikata aiyukkan ta’addanci a can baya.

 • Wane tasiri shirin RFJ yake da shi?

  Wane tasiri shirin RFJ yake da shi?

  • Ta hanyar aiki da shirin RFJ ne wasu kafofi suka bada bayanan da suka taimaka wajen hanawa ko warware wasu shirye-shiryen kai farmakin ta’addanci akan kadarorin Amurka da kuma cafke wasu daga cikkn ‘yan ta’adda mafi hatsari a duniya. Wannan hobbasar ta taimaka wajen ceton daruruwan rayukkan mutane.

   Alal misali, a Iraq, bayan kwannaki 18 da bada sanarwar goron tukuicin da za’a bada ne wani ya fito da bayanan da suka taimaka har aka gano inda Uday da Qusay Hussein suke. Wata babbar nasara da aka samu itace wacce ta kai ga cafke Ramzi Yousef, daya daga cikin wadanda suka kai harin shekarar 1993 akan Cibiyar Ciniki ta Duniya, wanda aka gano shi a shekrar 1995 a sanadin bayanin da wani ya bada bayan sanarwar bada goron tukuici da RFJ tayi.

 • Ta wace hanya kuke tallata tayin bada goron tukuici?

  Ta wace hanya kuke tallata tayin bada goron tukuici?

  • Ko bayan shafin RFJ, muna kuma anfani da sanarwowi masu hotuna, kwalayen ashana da tallace-tallace a gidajen radio da jaridu, duniyar gizo da duk wasu kafofin da suka cancanta wajen farauto masu kaiwa Amurka hare-haren ta’addanci.

 • Wane irin bayani ne kuke bayarwa gameda tukicin kudade da ake bayarwa?

  Wane irin bayani ne kuke bayarwa gameda tukicin kudade da ake bayarwa?

  • Wani muhimmin abu gameda wannan shirin shine cewa muna daukan matakan tabattarda cewa mun rufe asirin dukkan bayanan da ake bamu. Kuma bama fadin sunayen mutanen da muke baiwa goron tukuicin, bama ma fadar cewa mun bada wannan tukucin a bainar jama’a. Amma a cikin manyan hare-hare, mukan fadi cewa mun biya tukuicin amma bama fadin wadanda aka baiwa tukuicin.

 • Zaka iya bada bayani gameda wasu daga cikin kyauttukkan tukuicin da aka taba bayarwa?

  Zaka iya bada bayani gameda wasu daga cikin kyauttukkan tukuicin da aka taba bayarwa?

  • Izuwa yanzu tukuici mafi girma da muka taba biya shine na Dala milyan 30 da aka baiwa wani da ya bada bayanin da ya kai ga inda Uday da Qusay suke.

   Sau hudu shirin RFJ yana tarukkan biyan goron tukuci a kasar Philippines. Na baya-bayan nan shine wanda aka yi a ran 7 ga watan Yunin 2007 inda aka biya jimillar Dala milyan 10. Kuma wannan shine goron tukuici mafi tsoka da aka taba biya a kasar Phillipnes tunda aka fara wannan shirin.

 • Ta yaya zamu san cewa kun biya irin wadanan kudaden na tukuici idan har baku bada misalin wadcanda kua biya ba?

  Ta yaya zamu san cewa kun biya irin wadanan kudaden na tukuici idan har baku bada misalin wadcanda kua biya ba?

  • Kamar yadda aka fada, jefi-jefi shirin RFJ yas kan bada takaitacciyar sanarwar bada tukuci wadanda suka shafi manyan hare-hare. Haka kuma, duk lokacinda aka bada wani babban tukuci, mukan bada bayanin asiri ga Majalisar Dokoki.

 • Me ake akfin a samu wannan tukuici? Wane irin bayani kuke nema?

  Me ake akfin a samu wannan tukuici? Wane irin bayani kuke nema?

  • Duk wanda ya bada wani bayanin da yasa aka shawo kan ko kuma aka hana kai hare-haren ta’addancin kasa da kasa akan Amurka ko ina a duniya zai iya samun wannan tukuici.

   Alal misali idan aka kama ko aka yanke hukunci akan akan wani dake shirin kai hari ko ya kai harin, to wanda ya bada wannan bayanin, za’a iya bashi goron tukuici.

   Haka kuma duk wanda ke da bayani akan mazaunin wani jigon ‘yan ta’adda ko ya san dan ta’adda dake cikin wata kungiyar ta’addanci ta kasa-da-kasa, shima zai iya samun wannan tukuici. Haka kuma za’a iya bada goron yukuici ga duk wanda ya bada bayani akan wani mutum ko kungiyar dake safarar miyagun ababan sha don samarda kuddaden gudanarda aiyukkan ta’addanci ko gudanarda aiyukkan kungiyar ko tallafa mata.

   Sai dai kuma Dokar da ta kafa shirin nan ta haramta bada goron tukuci ga ma’aikatun gwamnatocin tarayya, jihohi, kananan hukumomi ko na kasashen waje da suka bada irin wadanan bayanan yayinda suke gudanarda aiyukkansu na yau da kullum.

 • Me zai faru idan wani ko wata suka yi kasadar bada wasu bayani akan wani Dan Ta’adda, daga baya suka gano cewa rayukkansu na cikin hatsari?

  Me zai faru idan wani ko wata suka yi kasadar bada wasu bayani akan wani Dan Ta’adda, daga baya suka gano cewa rayukkansu na cikin hatsari?

  • Kamar yadda aka fada a baya, rufin asiri wani muhimmin bangare ne na wannan shirin na RFJ. Shirin RFJ na rufe asirin duk bayanan da wani ko wasu suka bada dangane da neman bayanin da aka yi; haka kuma ana rufe asirin sunayen mutanen da aka baiwa goron tukuicin. Haka kuma ana iya sauya mazaunin wadanda suka bada bayanan tareda iyalinsu koda yake wannan ya kan danganta ne akan irin abinda ake aiki a kai.

 • Ta yaya ake biyan mutane?

  Ta yaya ake biyan mutane?

  • Duk tayin bada tukuicin da aka kawo, ana duba shi ne akan abinda ake aiki a kansa. Ga dai hanyoyin da ake bi wajen biyan wannan goron na tukuici:

   Da afrko dole ne wata ma’aikata ta Amurka dake gudanarda binciken kamar Ma’aikatar Tsaro, Hukumar FBI ko wani Opishin Jakadancin Amurka a wata kasar waje, su gabatarda sunayen mutumen da suke son a baiwa wannan tukuicin. Daga nan sai wata cibiyar ma’aikatu ta zauna tayi nazari akan tayin bada tukuicin. Idan Kwamitin Bada Tukucin Ma’aikatun yaga cewa bada wannan tukuicin ya dace, sai ya bada shawarar a bada tukucin ga Sakataren harakokin Wajen Amurka don neman amincewarsa na a bada tukuicin.

   Sai dai ba dole bane a yi aiki da shawarar da Kwamitin ya bada. Sakataren Harakokin Wajen Amurka nada cikakken ikon daukar matakin da yake so gameda tukucin kuma yana iya sauya yawan kudin da a’a biya ta hanyar aiki da abinda doka ta tanada.

   Idan akwai batun shara’a na tarayya gameda wani laifi da aka aikata a cikin lamarin, sakataren zai nemi yardar Atone-Janar kafin a biya tukuicin.

 • Ta yaya ake sanin yawan kudaden da za’a biya?

  Ta yaya ake sanin yawan kudaden da za’a biya?

  • Kaidojin biyan tukuicin sun dogara akan abubuwa da dama da suka hada, amma ba’a takaita kadai ga irin nau’in barazanar wani dan ta’adda ba, ko munin barazaar ga lafiyar Amurkawa ko kadarorin Amurka, darajar bayanin da aka bada, hatsarin da mai bada bayanin da uyalinsa ke iya fuskanta da kuma yawan hadin kan da shi mai bada bayanin ya bayar a wajen bincike ko shara’ar ‘yan ta’addan.

 • Shin shirin RFJ ya taba cire sunan wani daga jerin wadanda ake bada tukuici don bada bayani a kansu? In an taba, wane ne kuma don me?

  Shin shirin RFJ ya taba cire sunan wani daga jerin wadanda ake bada tukuici don bada bayani a kansu? In an taba, wane ne kuma don me?

  • Eh, lalle shirin RFJ ya sha cire sunayen mutane da dama da ake tuhuma a cikin shekarun da suka gabata, ciki harda Baitullah Mehsud, mai kai harin Bam na Bali Dulmatin, Usama Bin Laden, Atiyah Abd al-Rahman da kuma Fazu Abdullahi Mohammed. Akan cire sunayen wadanda ake tuhuma daga shirin na RFJ akan dalilai da dama da suka hada da idan ma’aikatan tsaro sun kama mutum ko idan wata Hukuma ta tabattarda cewa wannan mutumen ya mutu.

 • Zaka iya bada bayani gameda Asusun Shirin Bada Tukuici Don Adalci?

  Zaka iya bada bayani gameda Asusun Shirin Bada Tukuici Don Adalci?

  • Shirin Bada Tukuici Don Adalci, shirin jikayi ne, ba na neman riba ba, kuma mai zaman kansa da ba na gwamnati ba da ya dace da Dokar 501(c)(3) wanda abinda kawai ya hada alakarsa da M’aikatar Harakokin Wajen Amurka shine kokarin shirin na nwma da kuma cafke ‘yan ta’addar dake zaune a cikin Amurka da Kasashen Ketare. Amurkawa masu zaman kansu ne suka kirkiro kuma suke gudanarda wannan Shirin na Bada Tukuici Don Adalci. Bayan harin 11 ga watan Satumba ne wannan rukunin na Amurkawa suka tuntubi Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka, suka nemi a basu iznin neman tarbaccen kudade daga wajen jama’a do su tallafa wa shirin na RFJ. Mun duba wannan bukatar kuma muka amince da wannan yunkurin na Shirin Bada Tukuici Don Adalci. Bayan yayi shekaru yana taimakawa tun bayan harin 11 ga watan Satumba ne aka wargaza shirin a watan Agustar 2008.

 • Ashe bada irin wannan tukuicin ba zai karfafa wa wasu su zama mafarautan mutane ba?

  Ashe bada irin wannan tukuicin ba zai karfafa wa wasu su zama mafarautan mutane ba?

  • Da kakkarfar murya muke jkira akan mafarauta da su gujewa neman kama ‘yan ta’adda; a maimakon haka shirin RFJ ya ka samarda goron tukuicin da yake baiwa masu basahi bayanin da zai baiwa hukumomin gwamnati damar nema da kama irin wadanan mutanen.

 • Idan ina son in bada wani bayani, wa zan tuntunba?

  Idan ina son in bada wani bayani, wa zan tuntunba?

  • Duk wanda ke da wani bayani zai iya tuntubar Opishin Tsaro na Yanki dake a cikin Opishin Jakadancin Amurka ko Opishin harakokin Tafiye-Tafiye mafi kusa ko Hukumar FBI ko kuma ta wannan hanyar tuntuba:

   Adreshin aika sako: RFJ, Washington DC 20522-0303, USA
   Lambar wayar tarho ta kyaua: 1-800-US-REWARDS
   Sakon email: [email protected]

 • Ina neman izninka na inyi amfani da abubuwa (hotunan) dake cikin shafinka na duniyar gizo ta internet a cikin bayanin da zan gabatar ko kasida ta.

  Ina neman izninka na inyi amfani da abubuwa (hotunan) dake cikin shafinka na duniyar gizo ta internet a cikin bayanin da zan gabatar ko kasida ta.

  • In dai ba an saka wani hanin anfani ba, dukkan bayanin dake cikin wannan shafin na internet na jama’a ne, don haka kowa na iya sake maimaita sho ko wallafa shi ko anfani da shi ta wasu hanyoyi ba tareda neman iznin shirin RFJ. Muna bukatar a ambaci sunan RFJ a matsayin inda aka samu bayanin, kuma duk wani hoto ko bayanai da aka bada, su ma muna bukatar a ta;allaka su da RFJ.

   Idan har aka nuna hanin anfani da wani hoto, zane ko dai wasu abubuwa, to dole ne a nemi iznin yi anfani da su daga wajen wadanda suka mallaki wadanan abubuwan. Kuma ya kamata ka san cewa Dokar Hana laifukka mai lamba 18 U.S.C. 713, ta haramta yin anfani da Hatimin Kasa na Amurka ta wasu hanyoyi da aka bayyana a cikin wannan Baben; saboda haka muna bada shawarar a tujtunbi lauyoyi kafin a yi anfani da Hatimin Kasa ta kowace hanya.