Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Abdul Zakir

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Abdu Rauf Zakir, wanda kuma aka sani da lakabin Qari Zakir, shine madugun shirya hare-haren kunar bakin wake kuma Kwamandan mayakan Haqqani dake lardunan Kabul, Takhar, Kunduz da Baghlan dake Afghanistan. Zakir ne ke da alhakin shirya horaswa kan fannonin da suka hada da anfani da kananan makamai da manyan makamai da nakiyoyin IEDs.

A cikin shekarar 2008 ne Zakir ya tuntubi shugaban Kungiyar Haqqani, watau Sirajuddin Haqqani, yana neman tallafin kudi don fadada tasiri da aiyukkan kungiyar a arewancin Afghanistan, kuma tun lokaacin ya zama na-hannun-damar Sirajuddin Haqqani. Ya sha taka rawa a cikin shirya da dama daga cikin manyan hare-haren kunar bakin wake da Kungiyar Haqqani take kaiwa, kuma yana cikin masu yanke shawara akan ko a ci gaba da aiwatarda shirye-shiryen kai manyan hare-haren da kananan kwamandoji ke tsarawa. Wasu daga cikin hare-haren da aka yi anfani da mutanen Zakir wajen kaisu sun hada da wadanda aka kai a shekarar 2010 akan sansanonin sojan kawance dake Salerno da Chapman; da harin da aka kai kan otel din Continental a cikin watan Yunin 2011 wanda ya kashe fararen hula 11 da ‘yansandan Afghanistan biyu; da harin da aka kai a watan Satumbar 2011 kan Opishin Jakadancin Amurka dake Kabul, wanda ya hallaka mutanen Afghanistan su 16, ciki harda akalla yara shidda.

A ran 5 ga watan Nuwambar 2012 ne Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka ta kaddamarda Abdul Rauf Zakir a matsayin Rikakken Dan Ta’adda na Duniya a karkashin Dokar Hukuma mai lamba 13224.

Ita dai Kungiyar Haqqani kungiyar ‘yan tsagera ce da Jalaluddin Haqqani, wani tsohon Kwamandan mayakan da aka yi a shekarun 1980s, wanda kuma yayi yaki akan Tarayyar Soviet, ya kafa ta. Kungiyar Haqqani tana da alaka da kungiyoyin Taliban na Afghanistan da kuma al-Qaida, kuma burinsu shine su kafa gwamnatin ‘yan Taliban a can Afghanistan. Ita Kungiyar Haqqani mazauninta yana a yankin Wziristan ta Arewa dake kasar Pakistan ne, kuma ta kan sha yawan kai hare-hare kan iyaka a yankin gabashin Afghanistan da kuma Kabul. Ana yi wa Kungiyar Haqqani kallon cewa itace kungiyar mafi muni wajen kai hare-hare akan Rununar Sojan tarbacce ta Duniya dake Afghanistan da ma su kansu sojan na Afghanistan.

Kungiyar Haqqani ta jima tana tsarawa kuma tana kai hare-hare da dama da sace Sojan Kawance na Duniya dake Afghanistan da kuma fararen hula da jami’an Afghanistan kansu. Wasu daga cikin hare-hare mafi muni da wannan kungiyar ta kai sun hada da wanda ta kai a kan otel din Continental dake Kabul a watan Yunin 2011 wanda ya hallaka mutane fararen hula 11 da ‘yansanda biyu na Afghanistan; da harin bam na cikin mota da ta kai a lardin Wardak na Afghanistan a watan Satumbar 2011, wanda ya raunana sojoji 77 na Amurka; da wani harin sa’oi 19 da ta kai akan Opishin Jakadancin Amurka da kuma kan Helkwatar Rundunar Tsaro ta Kasa-da-Kasa (ISAF) dake Kabul a watan Satumbar 2011; da harin kunar bakin waken da ta kai a watan Yunin 2012 akan Barikin “Forward Base” dake Saelrno, inda sojoji biyu na Amurka suka rasa rayukkansu, yayinda sama da 100 suka sami rauni; da kuma mamayewar sa’oi 12 da ta yi wa otel din Spozhmai dake Kabul a watan Yunin 2012, wanda ya janyo mutuwar mutanen Afghanistan akalla 18, cikinsu harda fararen hula su 14.

A ran 19 ga watan Satumbar 2012 ne Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka ta kaddamarda Kungiyar Haqqani a matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda ta Kasashen Waje.