Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Abdul Rahman Yasin

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Taimakon kai tsaye Abdul Rahaman Yasin ya baiwa babban jigo Ramzi Ahmed Yousef wajen kai harin bama-bammai akan Cibiyar Ciniki ta Duniya dake New York a shekarar 1993. Yousef da Yasin sun tuka wata mota da aka shake da nakiyoyi zuwa karkashin ginin Cibiyar Cinikin ta Duniya, inda kuma karshenta mutane shidda suka rasa rayukkansu, wasu fiye da dubu suka ji raunukka. Yasin ya arce ya fice Amurka jim kadan bayan kai harin don kada a kama shi.

Bayan kai harin bama-bamman ne, ma’aikatan hukuma suka sami shedar da aka sa aka uhumci kuma aka kama mutane da yawa da ake zargi da taka rawa a cikin kai harin, ciki har da shi Yasin.

A Amurka aka haifi Yasin, daga baya ya koma Iraq da zama a shekarun 1960s, sannan kuma ya sake dawowa Amurka a bazarar 1992. Yana da fasfo na Amurka.

Ana tuhumar wannan mutum da aka nuna a sama da wadanan laifukkan:

Lalatawa ta hanyar anfani da wuta ko wani makamashi mai fashewa; lalata wata kadara ta Amurka ta hanyar anfani da wuta ko wani abin fashewa; sufurin nakiyoyi akan manyan hanyoyi; lalata motoci ko wurin motoci; makiricin aikata laifi ko zambatar Amurka; bada tallafi da taimako; hukuncin kisa ko daurin rai da rai idan har anyi asarar wata rayuwa; kai ma ma’aikcin hukuma hari a lokacinda yake bisa aiki; da kuma aikata laifi ta hanyar anfani da laifin tada hankali da anfani da mugun makami ko wani maganidisu.

Karin Hotuna

Abdul Rahman Yasin