Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Abdul Wali

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 3

Abdu Wali shine shugaban Jamaat ul-Ahrar (JuA), wani ɓangaren ‘yan ta’adda wanda ke da alaƙa da Tehrik-e-Taliban Pakistan (TTP). An bayar da rahoto cewa yana gudanar da ayyukansa daga Gundumomin Nangarhar da Kunar na Afghanistan.

A ƙarƙashin shugabancin Wali, JuA ta zamo ɗaya daga cikin ɓangarorin TTP da suka fi aikace-aikace a gundumar Punjab kuma ya furta gudanar da hare-haren ƙunar-baƙin-wake da sauran hare-hare a duk faɗin Pakistan.

A watan Maris 2016, JuA ta ƙaddamar da ƙunar-baƙin-wake a wurin taruwar jama’a a Lahore, Pakistan wanda ya hallaka mutane 75 kuma ya jikkata 340.

A watan Agusta 2015, JuA ta ɗaukin alhakin ƙunar-baƙi-wake a Punjab wanda ya hallaka Ministan Cikin Gida na Punjab Shuja Khanzada da magoya bayansa 18.

Wali kuma an san shi da Omar Khalid Khorasani. An haife shi a Hukumar Mohmand, Pakistan kuma an yi Imani cewa ya na cikin shekarunsa na 30. Tsohon ɗan jarida ne kuma marubucin waƙoƙi sannan ya yi karatu a wasu makarantu na madrasa a cikin Karachi.

Karin Hotuna

Abdul Wali