Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Abdul Saboor

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 3

Abdul Saboor kwararren masanin nakiyoyi ne dake da alaka da Hez-e Islami Gulbuddin (HIG).

Saboor ne ummul-haba’isin farmakin bam din kunar bakin waken nan na (SVBIED) ran 16 ga watan Mayun, 2013 da ya tashi daga cikin wata mota a Kabul, Afghanistan, wanda ya nakkasa wata motar tankin SUV ta sojan Amurka, wanda kuma ya hallaka sojan Amurka biyu da Amurkawa fararen hula guda hudu ‘yan kwangila da kuma ‘yan Afghanistan takwas – da suka hada da kananan yara guda biyu – kuma ya raunana wasu mutane 37.

Saboor ne da kwararren masanin nakiyoyin HIG Abdullah Nowbahar suka taka babbar rawa wajen harin bam na SVBIED da aka kai ran 18 ga watan Satumbar 2012 akan wata motar safa dake dauke da ma’aikatan Babban Filin Jirgin Saman Kabul, wanda kuma aka hallaka mutane fiyeda goma sha-biyu a cikinsa.