Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Abderraouf Ben Habib Jdey

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Abderraouf Jdey, wanda kuma aka sani da sunan Farouq al-Tunisi, mutm ne dake da tarihi na zama mai alaka da kungiyoyi masu matsanancin ra’ayi matuka. Ya jima yana da dangantaka ta kut-da-kut da kungiyar al-Qaida kuma ya sha yin hannu wajen sace-sace da aiyukkan kai hare-hare barkattai. Jdey mukkarabin Faker Boussora ne, dan kasar Tunisia da ake tuhuma da ta’addanci, kuma mai yiyuwa ne su biyun sun sha yin tafiye-tafiye tareda juna.

A shekarar 1991 n Jdey ya bar kasarshi ta bhaihuwa Tunisia yayi kaura zuwa birnin Montreal na Canada inda kuma, a shekarar 1995, ya zama dan kasar ta Canada. A lokacinda yake zaune a Canada ne Jdey yayi nazarin fannin hallita a Jami’ar Montreal kuma ya kan je Masallacin Assuna dake nan Montreal.

Jdey ya bar Canada a shekarar 1999, ya je Aghanistan inda, har zuwa shekarar 2000, yana karbar horaswa akan hanyoyin yaki daban-daban. Yana cikin wadanda suka yaki mayakan Kungiyar Hadin Gwaiwa na Arewancin Afghanistan (ko ANA) kuma ya taba rubuta wata wasikar kunar-bakin wake inda a ciki ya bayyana niyyarsa na mutuwar “Shahada” a cikin Jihadi. A wannan lokacin ne kuma Jdayi ya shiga cikin faifan bidio na ‘yan Shahada da aka shirya, wanda kuma, daga baya aka zo aka samu a gidan wani jigon ‘yan al’Qaida a shekarar 2001.

Bayan ya dawo ne a Montreal a shekarar 2001, wacce a cikinta ne yayi cudanya da mutane masu matsanancin ra’ayi kan hanyoyin yin Jihadi, karshenta Jdey ya bar Canada, Sai dai hukumomi na ci gaba da zama ciin damuar watakila Jdey zai iya dawowa Canada ko Amurka ya shirya ko kuma ya shiga wasu masu shirn kai hare-haren ta’addanci.

Karin Hotuna

Karin Hoton Abderraouf Ben Habib Jdey
Karin Hoton Abderraouf Ben Habib Jdey