Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Abdelbasit Alhaj Alhassan Haj Hamad

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

A ran 1 ga watan janairun 2008 ne aka harbe kuma aka kashe Ba’Murke kuma ma’aikacin Hukumar Raya Kasa ta Amurka (USAID) John Granville da direbansa dan kasar Sudan, Abdelrahman Abbas rahama a lokacinda suke kan hanyarsu ta komawa gida bayan bikin Jajibirin Sabuwar Shekara da suka halarta a Khartoum, Sudan. Granville, dan shekaru 33 da haihuwa, daman yana aiki ne akan karfafa demokradiya da mulki a Sudan. Shi kuma Abbas, dan shekaru 39 da haihuwa, ya soma aiki da USAID ne a shekarar 2004 a cikin Reshenta na Bada Agajin Gaggawa na Darfur. A rarrabe, kungiyoyi biyu suka dauki alhakin kai wannan harin: Ansar al-Tawhid (Magoya bayan Akidar Kadaicin Allah Guda) da kuma al-Qaida a Kasar Tapkunan Nilu Biyu (AQTN)

Hukumomin shara’ar Sudan sunyi wa mutane biyar shara’a kuma sun yanke musu hukunci akan rawar da suka taka cikin wadanan kashe-kashen. An yanke hukuncin kisa ta hanyar ratayewa akan Abu Zaid Mohamed Hamza, Mohamed Makawi Ibrahim Mohamed, Abdelbasit Alhaj Alhassan Haj Abdelraouf Hamad, da kuma Mohanad Osman Yousif Mohamed, sai dai kuma sun gudu shekara daya bayan yanke musu hukuncin. Mohanad ya rasu ne a Somalia cikin watan mayun 2011, shi kuma Abdeltaouf hukumomi sun sake cafke shi daga baya. Har yanzu ba’a kama Makawi da Abdelbasit ba.

Abdelbasit shine maharbi na biyu a kashe-kashen. A ran 11 ga watan Yunin 2010 ya gudu daga Gidan Yarin Khobar dake Khartoum, kuma yanzu haka yana Somalia.