Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Kwanton bauna a Niger a shekarar 2017

Tongo Tongo, Niger | 4 ga watan Oktoba 2017

Ranar 4 ga watan Oktoba 2017, wasu mayaka yan ta’adda masu dasawa da kungiyar Daular Islamiya a Babban yankin Sahara (ISGS), sun kai wani hari na kwanton bauna ga wasu zaratan sojoji na musamman na Amurka da ke girke a Niger domin gudanarda ayyukan bada horo, shawarwari da taimakama rundunar mayakan Niger a cikin aikinta na yaki da ayyukan ta’addanci, da kuma kawayensu sojojin Niger a kusa da kauyen Tongo Tongo a Niger iyaka da kasar Mali. Harin na kungiyar ISIS-GS ya yi sanadiyar mutuwar sojoji hudu aifafin kasar Amurka da wasu sojoji hudu yan kasar Niger. Bugu da kari, wasu sojoji Amurkawa biyu da wasu karin sojoji takwas yan Niger, sun jakkatta a cikin harin. A ranar 12 ga watan Janairun 2018, Adnan Abu Walid al-Sahraoui, shugaban kungiyar ISIS-GS ya yi ikirarin daukar alhakin kai wannan hari.

Tsarin Tukwici domin bayyanar gaskiya, ya tanadi bada wata ladar tsabar kudi da ba za su kasa da miliyan biyar na Dalar Amurka ba ga duka wanda ya bayarda labarinda za shi iya taimakawa ga cafkewa tare da gurfanarda duka mutumen da ke da alhakin wannan aika-aika na ta’addanci.

Mamatta

SFC Jeremiah Johnson de Springboro, daga jihar Ohio
SFC Jeremiah Johnson de Springboro, daga jihar Ohio
SSG Bryan Black de Puyallup, daga Washington
SSG Bryan Black de Puyallup, daga Washington
SSG Dustin Wright de Lyon, daga Georgia
SSG Dustin Wright de Lyon, daga Georgia
SGT La David Johnson de Miami Gardens, daga Florida
SGT La David Johnson de Miami Gardens, daga Florida