Labarai da Dumi-Duminsu

Qasim al-Rimi

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 10

An nada Qasim al-Rimi Emiyan AQAP, cikin watan Yuni na shekarar 2015, nan take bayan yayi rantsuwar hadin gwiwa da shugaban kungiyar al-Qa’ida Ayman al-Zawahiri kuma yayi kira da a sabunta kai hare-hare ga kasar Amurka. Al-Rimi ya horar da ‘yanta’adda a sansanin kungiyar al-Qa’ida dake kasar Afghanistan a cikin shekarun 1990, kuma daga baya ya koma kasar Yemen inda ya zama kwamandan sojan kungiyar AQAP. An yanke mashi hukuncin zama gidan yari na tsawon shekaru biyar a kasar Yemen cikin shekara ta 2005, kan laifin kitsa kashe Jakadan kasar Amurka, kuma ya gudu a cikin shekara ta 2006. An alakanta Al-Rimi da harin da aka kai ma ofishin Jakadancin Amurka dake Sana’a a cikin shekara ta 2008, wanda yayi sanadiyyar mutuwar wasu masu gadi ‘yan kasar Yemen su 10, da farar hula hudu, da wasu ‘yan ta’adda shidda. An kuma alakanta Al-Rimi da wani harin kunar bakin wake na “dan kamfai” da Umar Farouq Abdulmutallab ya so kaddamarwa a cikin wani jirgin saman kasar Amurka a cikin watan Disamba na shekarar 2009. Acikin shekara ta 2009, gwamnatin kasar Yemen ta zarge shi da gudanar da wani sansanin horarwar kungiyar al-Qa’ida a gundumar Abyan na kasar Yemen.

(Cikakken Bayani »)

Khalid Saeed al-Batarfi

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Khalid al-Batarfi babban dan kungiyar AQAP ne a Handramaut ta kasar Yemen kuma tsohon dan majalisar shura ne ta kungiayr AQAP. Acikin shekarar 1999, yayi tafiya zuwa kasar Afghanistan, inda yayi aikin horarwa a sansanin al-Farouq na al-Qa’ida. Acikin shekarar 2001, ya yaki sojojin Amurka da Sojan Kawance na Arewaci (Northern Alliance), tare da ‘yan kungiyar Talban, a cikin shekara ta 2010, al-batarfi ya shiga kungiyar AQAP a kasar Yemen, ya jagoranci mayakan AQAP wurin kame gundumar Abyan dake Yemen, kuma aka nada shi Emiyan AQAP na Abyan. Bayan mutuwar shugaban AQAP Nasir al-Wuhayshi a wani harin sama na sojojin Amurka cikin watan Yuni na shekarar 2016, ya samar da wani bayanin dake gargadin cewa al-Qa’ida zata ragargaza tattalin arzikin kasar Amurka da sauran ra’ayoyinta.

(Cikakken Bayani »)

Abdullah Ahmed Abdullah

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 10

Abdullah babban shugaban ne na yan al-Qaida, kuma shi memba ne na shugabancin majalisan al-Qa’ida, “majlis al-shura.” Abdullah na da kwarewa a jami’in sha’anin kudi,malami da kuma mai sarrafa dabara na al-Qa’ida.

Baban juri na tarayya a watan Nuwamba 1998 ta tuhumance da kuma caja Abdallah don matsayin shi a tashe-tashen bam a ranar bakwai ga watan Agusta,shekaran dubu goma shatara da tamanin da takwas (August 7,1998) a ofishin jakadanci na Amirka da suke Dar es Salaam, Tanzania a kuma Nairobi, Kenya. Kai farmaki ya kashe yan farar hula guda dari biyu da ishirin da hudu (224), fiye da dubu biyar (5,000) kuma sun samu rauni.

(Cikakken Bayani »)

Sayf al-Adl

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 10

Al-Adl an nuna shi da kuma caja shi a babban jurin tarayya a watan Nuwamba 1998 tadon matsayin shi a tashe-tashen bam a ranar bakwai ga watan Agusta,shekaran dubu goma shatara da tamanin da takwas (August 7,1998) a ofishin jakadanci na Amirka da suke Dar es Salaam, Tanzania a kuma Nairobi, Kenya. Kai farmaki ya kashe yan farar hula guda dari biyu da ishirin da hudu (224), fiye da dubu biyar (5,000) kuma sun samu rauni.

Shi Laftanan kanar ne ada tare da runduna na musamman na Egyptian kamin aka karma Shi a shekaran dubu goma sha tara da tasa’in da akwai (1987) tare da dubbai tsagera yan adawa da gwannatin kasa biye da kokarin kis an gilla na ministan harkokin cikin Egypt.

Kamar lokacin farkon dubu goma sha tara da tamanin,al-Adl da sauran yan ma’aikacin al-Qa’ida sun da da koyarwa na soja da basira a kasashe daban-daban,harda Afghanistan, Pakistan da Sudan,don amfani na al-Qa’ida tare da rukunin alakar su, da jihadi musuluncin Egyptian.

(Cikakken Bayani »)

Abdul Wali

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 3

Abdu Wali shine shugaban Jamaat ul-Ahrar (JuA), wani ɓangaren ‘yan ta’adda wanda ke da alaƙa da Tehrik-e-Taliban Pakistan (TTP). An bayar da rahoto cewa yana gudanar da ayyukansa daga Gundumomin Nangarhar da Kunar na Afghanistan.

A ƙarƙashin shugabancin Wali, JuA ta zamo ɗaya daga cikin ɓangarorin TTP da suka fi aikace-aikace a gundumar Punjab kuma ya furta gudanar da hare-haren ƙunar-baƙin-wake da sauran hare-hare a duk faɗin Pakistan.

A watan Maris 2016, JuA ta ƙaddamar da ƙunar-baƙin-wake a wurin taruwar jama’a a Lahore, Pakistan wanda ya hallaka mutane 75 kuma ya jikkata 340.

(Cikakken Bayani »)

Mangal Bagh

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 3

Mangal Bagh shine shugaban Lashkar-e-Islam, wani ɓangaren ‘yan ta’adda wanda ke da alaƙa da Tehrik-e-Taliban Pakistan (TTP). Ƙungiyarsa na samun kuɗin shiga daga fataucin ƙwayoyi, fasa-ƙwauri, satar jama’a, hare-hare a kan Tawagar Ƙungiyar Tarayyar Turai, da kuma haraji a kan kasuwanci tsakanin Pakistan da Afghanistan.

Bagh ya jagoranci Lashkar-e-Islam tun 2006 kuma daga lokaci zuwa lokaci ya canza ƙawancensa domin kare kuɗaɗen shiga na haram a ƙarƙashinsu yayin da yake tilasta nau’in Musulunci na Deobandi Islam a yankunan gabacin Afghanistan da yammacin Pakistan waɗanda yake da iko da su musamman Gundumar Nangarhar, Afghanistan.

Wanda aka haifa a Hukumar Khyber, Pakistan, an yi Imani cewa ya na cikin tsakiyar shekarunsa na arba’in. Bagh ɗan ƙabilar Afridi ne. Yayi karatu a makarantun madrasa na shekaru masu dama kafin daga bisani ya yi faɗa tare da ƙungiyoyin sa kai a Afghanistan.

(Cikakken Bayani »)

Ahlam Ahmad al-Tamimi

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

‘Yar kasar Jordan, Ahlam Ahmad al-Tamimi, wanda kuma aka sani da suna “Khalti” da “Halati,” wani dan ta’addan kungiyar HAMAS ne da ke fuskantar shari’a.

A ranar 9 ga Ogosta, 2001, al-Tamimi ya yi jigilar wani bom da wani dan kunar bakin waken kungiyar zuwa wani wurin dake da cunkuson mutane a Ebarro pizzeria dakeJerussalam HAMAS, inda dan kunar bakin waken ya tayar da bom din wanda ya kashe mutane 15, ciki har da yara bakwai. An kashe Amurkawa biyu a cikin harin – Judith Shoshana Greenbaum, wata malamar makaranta mai shekaru 31 mai juna biyu, daga jihar New Jersey, da Malka Chana Roth, wani yaro mai shekaru15. Sama da mutane 120 suka raunata, wadanda suka hada da wsu Amurkaw hudu. Kungiyar HAMAS ta ce ita ke da alhakin kai harin

(Cikakken Bayani »)

Talal Hamiyah

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 7

Talal Hamiyah shine shugaban Ƙungiyar Tsaron Waje ta Hizballah (ESO), wacce ke kula da shiryayyun gidajen kurkuku a faɗin duniya. ESO itace shashi mai ɗaukar nauyin shiryawa, tsarawa da aiwatar da hare-haren ta’addanci a wajen Lebanon. Ana kai waɗannan hare-haren musamman a kan Isra’ilawa da Amurkawa.

Shashin Ma’ajiya na Amurka ya ambaci Talal Hamiyah a ranar 13 ga Watan Satumba, 2012 a matsayin Babban Ɗan Ta’adda na Duniya (SDGT) domin bin Dokar Gwamnati ta 13224 ta bayar da tallafi a kan ayyukan ta’addanci zuwa ga Hizballah a Gabas ta Tsakiya da sauran duniya.

(Cikakken Bayani »)

Fuad Shukr

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Talal Hamiyah shine shugaban Ƙungiyar Tsaron Waje ta Hizballah (ESO), wacce ke kula da shiryayyun gidajen kurkuku a faɗin duniya. ESO itace shashi mai ɗaukar nauyin shiryawa, tsarawa da aiwatar da hare-haren ta’addanci a wajen Lebanon. Ana kai waɗannan hare-haren musamman a kan Isra’ilawa da Amurkawa.

Shashin Ma’ajiya na Amurka ya ambaci Talal Hamiyah a ranar 13 ga Watan Satumba, 2012 a matsayin Babban Ɗan Ta’adda na Duniya (SDGT) domin bin Dokar Gwamnati ta 13224 ta bayar da tallafi a kan ayyukan ta’addanci zuwa ga Hizballah a Gabas ta Tsakiya da sauran duniya.

(Cikakken Bayani »)

Muhammad al-Jawlani

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 10

Muhammad al-Jawlani, wanda kuma aka sani da Muhammad al-Golani, wanda kuma aka sani da Muhammad al-Julani, babban jagora ne na ƙungiyar ta’addanci, wato al-Nusrah Front (ANF), reshen Syria na al-Qa’ida. A watan Aprilu, al-Jawlani ya yi mubaya’a ga al-Qa’ida da kuma jagoranta Ayman al-Zawahiri. A watan Yuli 2016, al-Jawlani ya yabawa al-Qa’ida da al-Zawahiri a wani faifan bidiyo na yanar gizo kuma ya yi iƙirari cewa ANF zata canza sunanta zuwa Jabhat Fath Al Sham (“Kame Filayen Daga”). A ƙarƙashin jagorancin al-Jawlani, ANF ta ƙaddamar da jerin hare-haren ta’addanci a Syria, wasu lokuta da suke harar fararen hula. A watan Aprilu na 2015, an bayar da rahoton cewa ANF ta sace mutane, kuma daga bisani ta saki a ƙalla fararan hula Ƙurdawa 300 daga wani wurin duba abuben hawa a Syria. A watan Yuni 2015, ANF ta ɗauki alhakin hallaka mutane 20 mazauna ƙauyen Druze na Qalb Lawzeh a gundumar Idlib, Syria. (Cikakken Bayani »)

Kisan Joel Wesley Shrum

Taizz, Yemen | 18 ga watan Maris, 2012

A ranar 18 ga watan Maris, 2012, Shrum, mai shekaru 29, aka harbe shi kuma aka kashe shi a kan hanyarsa ta zuwa aiki a Taizz, Yemen, wanda wani ɗan bindiga da ke kan babur ya tsaya kusa da abin hawansa ya aikata. A lokacin rasuwarsa, Shrum yana aiki a Cibiyar Horo da Ci gaba Ta ƙasa-da-ƙasa a matsayin jami’i kuma malamin Turanci. Yana zaune a Yemen tare da matarsa da ƙananan yara guda biyu. Kwanaki kaɗan bayan harin, ƙungiyar ta’addanci ta al-Qaida dake Shashin Larabawa (AQAP) ta yi iƙirarin ɗaukan alhakin kisan. Shirin Bayar da lada na Shashin Ƙasa kan Sakayya Domin Tabbatar da Adalci na Amurka yana ba da lada har zuwa Dala miliyan 5 domin bayani da zai kai ga kamawa ko amincewa da laifi na mutanen da suka aikata, tsara, ko taimakawa wajen kisan Ba’amurke Joel Shrum. (Cikakken Bayani »)

Abu Bakr al-Baghdadi

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 25

Abu Bakr al-Baghdadi, wanda har wa yau aka san shi da lakabin Abu Du’a, da kuma lakabin Ibrahim ‘Awwad Ibrahim ‘Ali al-Badri, shine babban shugaban kungiyar ta’addanci ta Isalama ta Iraq da Levant (ISIL). Barazanar al-Baghdadi ta dada karuwa tun daga shekarar 2011, lokacin da Ma’aikatar Harakokin Waje tayi sanarwar bada goron Dala Milyan 10 ga duk wanda ya bada bayanin da ya kai ga inda yake, kama shi ko kuma kai ga yanke mishi hukunci. A cikin watan Yunin 2014 ne kungiyar ISIL, (wacce kuma aka sani da sunan Da’esh) ta kama sassa daban-daban a kasashen Syria da Iraq, ta girka mulkin Islamiyya kuma ta nada al-Baghdadi a matsayin shugaban addini na wuraren. A shekarun da suka gabata, ISIL ta sami mubayi’ar kungiyoyin ‘yan jihadi da dama da kuma nasarar cusawa mutane akidar addini mai tsanani a kasashen duniya daban-daban, ta kuma karfafa gwiwar a rinka kai hare-hare akan Amurka. (Cikakken Bayani »)

Gulmurod Khalimov

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 3

Tsohon Kanar na Sojan Tajikistan, kwamandan ‘yansanda, gwanin harbi na soja, Gulmurod Khalimov, jami’in Kungiyar ‘yan Islama ta ISIL ta Iraq da Levant ne kuma mai daukar mata ma’aikata. Shi ne babban kwamnadan wata bataliyar soja ta musamman da aka kafa a cikin Ma’aikatar Harakokin Cikin Gida ta Tajikistan. Khalimov ya taba fitowa cikin wani faifan bidiyon farfaganda da aka yi, inda aka ganshi yana tabattarda cewa lalle shi mayakin ISIL ne kuma har, a bainar jama’a, yana kira ga a kai wa Amurkawa farmaki na ta’addanci. (Cikakken Bayani »)

Abu-Muhammad al-Shimali

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Tun cikin shekarar 2005 ake alakanta Tirad al-Jarba da aka fi sani da lakabin Abu-Muhammad al-Shimali, wanda kuma shine Shugaban Harakokin Kan Iyakoki na Kungiyar Al’ummar Islama ta Iraq da Levant (ISIL) da ita kungiyar ta ISIL, wacce a can da aka sani da sunan al-Qaida a Iraq. Yanzu haka shine yake jagorancin aiyukkan da suka danganci Shige da Fice da kuma Samarda Kayan Aikin (Cikakken Bayani »)

Fasa-Kwabrin Kayan Tarihi da na Mai dake anfanar Kungiyar Islama ta Iraq da Levant (ISIL)

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada ladar da zata kai har Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga tsaida saye ko sayarda mai da kayan tarihi da ake don anfani, ko da sunan, ko a madadin kungiyar ‘yan ta’addar nan ta ‘yan kishin Islama (ISIL) ta Iraq da Levant wacce kuma aka sani da lakabinta na Larabci, watau DAESH. (Cikakken Bayani »)