Dandalin Yanar Gizo na Gwamnatin Amurka a hukumance

Game da mu

Tambayoyin da Ake Yawan Yi

RFJ shiri ne na gamayyar hukumomi na ba da lada da an kafa shi bisa Dokar Yaƙi da Ta’addanci a Ƙasashe ta 1984, dokar Public Law 98-533 (mai laƙabin 22 U.S.C.§ 2708) wanda kuma Sashen Tsaro na Difilomasiyyar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ke gudanarwa.    

Manufar RFJ ita ce tattara bayanan da za su taimaka wajen inganta tsaron Amurka.

Ƙarƙashin ikonta na 1984, manufar RFJta ainihi ita ce ba da lada kan bayanan da za su

  • Kai ga kamawa da gurfanar da duk wani mutum da ya shirya, ko ya aikata, ko ya taimaka, ko ya yi yunƙurin aikata ta’addanci a ƙasashen duniya kan Amurkawa ko kadarorin Amurka.
  • Daƙile faruwar irin waɗannan ayyuka takamaimai
  • Kaiwa ga tantance wani jagoran ta’addanci ko gano inda yake
  • Daƙile ɗaukar nauyin ta’addanci 

 

A 2017, Majalisa ta yi wa ikon dokar RFJ gyara, inda ya ƙunshi ba da lada kan bayanan da suka kai ga

  • Daƙile hanyoyin samar da kuɗin ɗaukar nauyin ta’addanci da wasu mutane ke yi ta wasu ayuka da ke tallafa wa gwmanatin Koriya ta Arewa
  • Tantance wani mutum wanda ke aiki bisa umarnin ko ƙarƙashin ikon gwamnatin wata ƙasa, yake taimakawa ko ƙarfafa wa wani gwiwa wajen karya Dokar Zamba ta Intanet (da ke aikata kutse da sauran laifukan da suka shafi kwamfuta) ko da turanci Computer Fraud and Abuse Act, ko kuma ko gano inda mutumen yake

 

Lada kan zama daga ƙasa dala Amurka miliyan ɗaya zuwa miliyan 25.  

RFJ ka iya biyan lada a wasu lokuta ko da kuwa ba ta yi tayi ba a baya.

Tun bayan kafa shi, RFJ ya biya kuɗaɗe da suka kai dalar Amurka miliyan 250 ga mutum fiye da 125 da suka ba da bayanai masu amfani da suka taimaka wajen kyautata tsaron Amurka.  

Waɗannan ƙoƙarce-ƙoƙarce sun taimaka wajen ceton rayukan mutane ba iyaka.

Ban da dandalin yanar gizon RFJ, muna amfani da harsuna daban-daban a shafukan sada zumunta, da fasta, kwalin ashana da sanarwa ta biya, da talla a rediyo da jaridu, da intanet da duk wata hanyar sadarwa da ta dace don zantawa da mutane da ƙila suke da bayanai masu muhimmanci da za su bayar.

Sirri abu ne mai muhimmi a shirin RFJ. Ba ma fitar da bayanai ƙarara da aka ba mu don neman lada ko kuma sunayen mutanen da suka karɓi ladan, kuma ba mu ma faɗa wa duniya cewa an ba da ladan. A wasu lokutta da suka shafi manyan lamuran, muna iya faɗar biyan lada amma ba da bayanan da aka bayar ba ko sunan wanda ya bayar.

A Fabarairun 1995, an gano da kuma kama ɗaya daga cikin maharan Cibiyar Kasuwanci ta Duniya Ramzi Yousef a Pakistan sakamakon bayanan da wani ya bayar bayan ya karɓi tayin ladan da RFJ ya yi.

Haka kuma, RFJ ya biya ladaddaki ga ɗaiɗaikun mutane a bainar jama’a sau huɗu a Philippines.  A ranar 7 ga watan Yunin 2007, RFJ ya bayar da ladan dalar Amurka miliyan 10 yayin wani biki a fili. Wannan shi ne lada mafi girma da RFJ ya taɓa bayarwa a Philippines tun baayan ƙaddamar da shirin. 

RFJ ya ba da ladan dalar Amurka miliyan 3 wa wani mutum da ya ba da bayanin da ya kai ga kamawa da gurfanar da jagoran ta’addanci Ahmed Abu Khattalah, jagoran harin 2012 kan ƙaramin ofishin jakadancin Amurka a Benghazi a Libya wanda ya kashe Amurkawa huɗu, ciki har da jakadan Amurkar.  

Kamar yadda aka bayyana, RFJ na bayyana wasu ƙayyadaddun bayanai kan biya da aka yi game da wasu shahararrun mutane.  

Kazalika, muna ba wa Majalisa rahoton biyan lada bayan an biya.

Mutane ka iya cancantar samun lada idan suka ba da bayanin da ya kai ga:

  • Taimakawa ko kuma yin nasarar warware ayyukan ta’addanci a ƙasashe da ake ƙulla wa Amurkawa ko kuma kadarorinsu a ko’ina a faɗin duniya.
  • Kaiwa ga tantance wani jagoran ta’addanci a wata ƙungiyar ta’addanci a ƙasar waje ko kuma gano inda yake.
  • Lalata shirin samar da kuɗaɗe na wasu mutane ko ƙungiyoyi da ke shiga wasu ayyuka na taimaka wa gwamnatin Koriya ta Arewa.
  • Kaiwa ga tantance ko kuma gano inda duk wani mutum yake, wanda a yayin da yake aiki ƙarƙashin umurnin gwamnatin wata ƙasa ko bisa jagorancin gwamnatin wata ƙasar waje ta taimakawa ko ƙarfafa gwiwar karya Dokar Zamba ta Intanet wato Computer Fraud and Abuse Act. 

 

Jami’an gwamnati ba su cancanci samun lada ba har sai idan sun ba da bayanan da ba su shafi ayyukansu na gwamnati ba a hukumance. 

Sirri abu ne mai muhimmi a shirin RFJ. RFJ na ɓoye bayanan wanda ya ba da bayanai baki ɗaya da kuma mutanen da suka samu lada. Bugu da ƙari, akwai yiwuwar sauya wa mutum da ma iyalinsa wurin zama ta hanyar duba yanayin lamarinsa.

Samun lada daga RFJ abu ne da ya ƙunshi matakai:

  • Dole ne sai wata hukumar bincike ta Amurka (kamar Ma’aikatar Tsaro ko FBI)) ko kuma wani ofishin jakadancin Amurka a ƙasar waje ya miƙa sunan mutum don samun lada. Mutanen da ke ganin sun ba da bayanai ba lallai ne su iya miƙa sunansu da kansu ba don karɓar lada.
  • Bayan duba cancanta ta hanyar shari’a, wani kwamatin haɗin gwiwar hukumomi zai tantance bayanan da wata hukuma ta miƙa. Bayan kammala tantance cancanta, sai kwamatin ya bai wa Sakataren Harkokin Waje shawara.
  • Sai dai ba dole ne a yi amfani da shawarar da kwamatin ya baayr ba. Sakataren Harkokin Waje ne ke da wuƙa da nama wajen yanke hukuncin ba da lada, kuma zai iya sauya adadin ladan cikin hurumin doka.
  • Kafin biyan lada a kan kowane irin lamari da ke cikin hurumin gwamnatin tarayya, wajbi ne sa lauya Atoni Janar ya amince da abin da Sakataren Harkokin Waje ya yanke.
  • Miƙa sunan mutum ba tabbas ba ne wajen samun lada. Tsaida shawarar Sakataren ita ce ta ƙarshe kuma kammalawa, sannan kuma ba sai wata kotu ta duba lamarin ba.

Ana ƙiyasta adadin ladan ta hanyar lura da abubuwa da dama, ciki har da: kimar bayanan da aka bayar;gwargwadon haɗarin da aka daƙile da bayanan;girman haɗarin da aka daƙile da ka iya shafar Amurkawa ko dukiya;haɗarin da wanda ya ba da bayanan ke ciki da danginsa;da kuma irin haɗin kan da mai ba da bayanan ya bayar.  Ba a ba da lada don mutum ya ba da shaida a gaban kotu. 

Adadin ladan da za a bai wa mai ba da bayanai ka iya kasancewa jimillar adadin dalar da aka tallata.

E, Lada Don Adalci ya cire sunayen waɗanda ake zargi da dama daga jerin sunaye tsawon shekaru, ciki har da shugaban al-Ƙa’ida Usama bin Ladin da shugaban ISIS Abu Bakr al-Baghdadi.  

Akan cire waɗanda ake zargi daga jerin shirin RFJ saboda dalilai daban-daban, ciki har da idan jami’an tsaro suka kama su, ko aka tabbatar da mutuwarsu, ko kuma idan aka tabbatar a hukumance cewa yanzu ba barazana suke ba. 

Ba ma son masu neman ɓagas da kuma waɗanda ba hukuma ba su shiga aikin kama ‘yan ta’adda ko kuma mutanen da ake nema ruwa-a-jallo;a madadin haka, RFJ na ba da lada saboda samun bayanan da za su taimaka wa hukumomin gwamnati ganowa da kuma kama irin waɗannan mutanen.

Mutanen da ke da bayanai su tura wa RFJ saƙo ta WhatsApp, ko Telegram, ko kuma ta +1 (202) 975-9195  

Mutane za su iya ba da bayanai ta hanyar tuntuɓar ofishin yanki a ofishin jakadancin Amurka mafi kusa, ko kuma ofishin FBI mafi kusa.

Bayanai a wannan shafin na jama’a ne kuma za a iya amfani da su a wani wajen, ko sake wallafawa ba tare da neman izinin RFJ ba har sai idan an ambaci haƙƙin mallaka. Muna buƙatar a ruwaito RFJ a matsayin majiyar bayanan sannan duk wani hoto da aka ɗauka da kuma wanda ya rubuta bayanin a bai wa mai shi haƙƙinsa yadda ya dace. 

Idan an rubuta haƙƙin mallaka a jikin hoto, ko wani zane, ko wani abu, wajibi ne a samu izini daga haƙiƙanin wanda ya mallake shi. Bugu da ƙari, ya kamata ku sani cewa wata dokar laifuka ta 18 U.S.C.713 ta haramta amfani da hatimin gwamnatin Amurka na Great Seal a kan wasu keɓantattun lamura;saboda muna shawartarku da ku tuntuɓi lauya kafin amfani da hatimin a ko’ina.

Sashen Tsaron Difilomasiyya Diplomatic Security Service (DSS) na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ne ke kula da shirin Lada Don Adalci. DSS ya saka wani ɓangare game da Lada Don Adalci a shafinsa: https://www.state.gov/rewards-for-justice/. Shafin kan kawo mutum kai-tsaye zuwa wannan shafin – na RFJ – don mutane su ba da bayanai.

SUBMIT A TIP

Do Your Part. Secure a Safer World.

There are many ways to submit information to Rewards for Justice.

You may choose from multiple platforms and contact us in numerous languages. To process your information efficiently, we ask you to state your information as succinctly as possible, provide your name, location, and preferred language, and upload all relevant files such as photographs, videos, and documents to support your information. An RFJ representative will soon contact you. Please be patient, as RFJ reads every tip we receive.

Please visit our Tor-based tips-reporting channel at: he5dybnt7sr6cm32xt77pazmtm65flqy6irivtflruqfc5ep7eiodiad.onion

Turo da Bayani

Ba da gudummawarku Samar da Duniya Mai Kwanciyar Hankali.

Akwai hanyoyi da yawa da za ku iya turo da bayani.

Za ku iya zaɓa daga wurare daban-daban kuma tuntuɓe mu a harsuna daban-daban. Don yin aiki da bayananku yadda ya kamata, muna buƙatarku da ku zayyana bayananku ƙarara, ku saka sunanku, da wurin da kuke, da harshen da kuka fi so, sannan ku ɗora dukkan takardun da suka dace, kamar ƙaramin hoto, da bidiyo da za su ƙarfafi bayanan naku. Jami’in shirin RFJ zai tuntuɓe ku nan gaba kaɗan. Muna roƙo da ku ƙara haƙuri saboda muna karanta dukkan bayanan da muka samu.

Muna roƙo ku buɗe manhajarku ta Signal don turo rahoto. Lambar ita ce +1 (202) 975-9195

Muna roƙo ku buɗe manhajarku ta Telegram don turo rahoto. Lambar ita ce +1 (202) 975-9195

Ku duba shafin da zai ba ku ƙarin bayani game da turo rahoto a: he5dybnt7sr6cm32xt77pazmtm65flqy6irivtflruqfc5ep7eiodiad.onion

Skip to content